Za Mu Dawo Da Darajar Arsenal, Inji WengerMai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Arsene Wenger, ya ce, dole ne kungiyar ta maido da magoya bayanta don ci gaba da karfafa mata gwiwa bayan ‘yan wasansa sun yi nasarar casa Watford da ci 3-0 a gasar firimiya ta Ingila jiya Lahadi duk da cewa dubban magoya bayan kungiyar sun kaurace wa kallon wasan a filin wasa na Fly Emirates.

Nasarar da Arsenal ta samu na zuwa ne bayan Arsenal din tasha kashi a wasanni uku da ta yi a jere a gasar ta firimiya, lamarin da ya janyo wa Mista Wenger caccaka daga magoya bayan kungiyar.

Kwallayen da Shkodran Mustafi da Pierre-Emerick Aubameyang da Henrikh Mkhitaryan suka zura sun bai wa Arsenal damar samun nasararta ta farko a gasar tun bayan lallasar da ta yi wa Eberton da ci 5-1 a ranar 3 ga watan Fabairu.

Wenger ya ce, babu shakka sun tsinci kansu a cikin tsaka mai wuya da ya ritsa da magoya bayansu, amma za su ci gaba da taka rawa don dadadawa magoya bayansu kamar yadda ya bayyana.

 

What's Your Reaction?

Angry Angry
0
Angry
Cute Cute
0
Cute
Fail Fail
0
Fail
Geeky Geeky
0
Geeky
Lol Lol
0
Lol
Love Love
0
Love
OMG OMG
0
OMG
Win Win
0
Win
WTF WTF
0
WTF

Comments 0

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Za Mu Dawo Da Darajar Arsenal, Inji Wenger

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format