Wani Mutum Mai Shekaru 63, Mai Mata 3 Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 2 FyadeKotu ta yankewa wani mutum mai shekaru 63 hukuncin daurin rai da rai a gidan yari bayan da ta kama shi da laifin yi wa yarinya ‘yar shekaru 2 fyade.

Mutumin ma suna Musa Mulo dai ya na da mata uku da yara da ba a bayyana adadin su ba.

Rahotanni sun bayyana cewa mutumin limami ne a masallacin Kibubbu da ke yanki Lugazi a jahar Uganda.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne dai bayan da Mulo ya amsa laifin shi.

KARANTA WANNAN: Uba ya hadu da dan shi sun yi wa ‘yar karamar ‘yar shi fyade (Hotuna)

Lauyan masu kara, Janet Kitimbo ta fadawa kotun yadda lamarin ya faru. Ta ce a ranar, yarinyar ta je gidan Mulo, wanda ke da makobtaka da na su. Da ganin ta, sai ya dauke ta ya shiga da ita daki inda ya aikata aika aikar, lamarin da ya haddasa raunatar gaban yarinyar.

Mahaifiyar yarinyar mai suna Misis Nalumasi ita ta kai kara wajen ‘yan sanda, inda daga bisani aka kama Mulo.

A lokacin, musulmin yankin su afka gidan Nalumasi inda suka farfasa mata kayayyaki bayan da suka zarge ta da yi wa limanim su kazafi.

Sai dai Mulo bai yi tamtama ba a kotu, inda ya amsa aikata laifin.

A cewar shi “Bayan na dauke ta na dora ta a kan cinya ta, kawai sai na ga zip din wando na ya na budewa da kan shi”

 

 

Post Views: 38

What's Your Reaction?

Angry Angry
0
Angry
Cute Cute
0
Cute
Fail Fail
0
Fail
Geeky Geeky
0
Geeky
Lol Lol
0
Lol
Love Love
0
Love
OMG OMG
0
OMG
Win Win
0
Win
WTF WTF
0
WTF

Comments 0

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Wani Mutum Mai Shekaru 63, Mai Mata 3 Ya Yi Wa ‘Yar Shekara 2 Fyade

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format