Siriya: Gargadi kan yada labaran bogi | Labarai | DW


Wani dan jarida mai suna Ahmad Primo dan asalin kasar Siriya da ya kafa kungiyar nan ta Verify-sy da ke aiki wajen tabbatar da sahihancin labarai da rahotanni ya ce dabi’ar yada labarai na karya a shafukan sada zumunta na intanet ba za ta amfanawa kasar da ma duniya komai ba illa cigaba da haifar da tashin hankali.

Wannan ne ma ya sanya Mr. Primo din yin kira ga takwarorinsa ‘yan jaridu da su tashi haikan wajen magance wannan dabi’a ta hanyar tantance labarai kafin su kai ga yada shi, hakan inji shi, shi ne zai kai ga kawo karshen matsalar fidda labaran bogi da yanzu haka ta zama ruwan dare.Source link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *