Riko Da Gaskiya Ne Sirrin Ci Gaban Sana’armu Na Sayar Da Gidaje -Sa’idu SambawaALHAJI SA’IDU BALA SAMBAWA shi ne mataimakin shugaban kungiyar masu bayar da gidaje haya da saye da sayarwa na karamar hukumar Sabon Garin Zariya kuma shi ne babban sakataren babban kasuwar Samaru duk a jihar Kaduna a wannan lokaci ya bayyana cewa gaskiya ita ce ginshikin duk wata nasara da kungiyarsu take samu a yayin da suke zantawa a ofishinsa da wakilinmu na Zariya IDRIS UMAR ya tattauna da shi, ga yadda tattaunawar tasu ta kasance.

Da farko masu karatu zasu so su ji tarihinka a bagaren wannan sana’ar taku ta bayar da hayan gidaje da sayen gida da sayarwa?

To jama’a kamar yadda kuka ji suna na Alhaji Sa’idu Bala Sambawa to tabbas haka ne kuma ni ne mataimakin shugaba basu bayar da haya a fadin karamar hukumar Sabon Gari kuma ni ne sakatare kasuwar Samaru kuma na fara wannan sana’ar ce akalla shekara 27 da suka gabata ya zuwa yanzu nasan hagu da damar wannan sana’ar babu abin da zai layence min tun daga karamar hukuma har zuwa jiha da tarayya Nijeriya baki daya .

To ko zaka iya gayawa masu karatu yadda sana’ar taku take ?

Kwarai kuwa, ita wannan sana’ar ta mu ta bayar da haya gida ga mai bukata ko nema wa wani gida ya saya ko bayar da shawara ga mai bukatar zuba jari a harkar gini ko sayan muhalli a gurin gwamnati ko wajen dan kasuwar ba wata sana’ace basuwa da mutane basu santa ba wannan sana’ar tun zamanin baya muna  da ita sai dai an sami ci gaba sosai don kauce wa shiga rigima, misali shi ne mu a yanzu ba zaka shiga kungiyarmu ba sai ka yi rijista ka sayi fom ka cika a cikin fom din akwai tambayoyi da zaka amsa da zasu nuna wa kungiyar kai mai gaskiya ne na biyu ita wannan kungiyar aikin ta shi ne kowa ke son hayan gida a ko a wani jiha a fadin kasan nan in har ya kawo mana cigiya to da yardan Allah zamu sama masa baya ga haka kuma akwai masu zuwa da damuwa suna son su sayi gida amma a waje mai daraja to mu kan bada shawara tare da nuna wa mutum wurare masu daraja ko kuma wani zai fara gini sai kudi su yanke masa to in yazo wajenmu zamu  iya karisa masa tare da yarjejeniya mai kyau in an gama za a sa ‘yan haya a ciki in sun biya sai mu cire kudin sa mu bashi mu kuma ya bamu namu baya ga haka kuma a halin yanzu manyan masu kudi suna da gidaje da suna son wanda zai kula masu da shi bisa amana to su kan zo wajen mu karba mu sama masu mai so amma wanda bincike ya tabbatar mana cewa lallai mai gaskiya ne.

Ya zuwa yanzu gwamnati ta san da zaman ku?

To ai inda gwamnati ba ta san da zaman mu ba to da nasarorin da muka sumu da bamu same shi ba don haka kungiyarmu na bai wa gwamnati goyan baya wajen tabbtar da mutane masu gaskiya ne ke gudanar da harkar bayarb da haya a jihar, muna kuma sanya ido a kan bata garin dake zuwa neman haya su kuma aikata laifi.

Akwai nasarorin da kuka kawo wa wannan sana’ar taku wanda zai gamsar da jama’ar dake tare damu?

Sosai kuwa daga ciki akwai dakile marasa gaskiyar cikin sana’ar tare da bada damar samar wa wasu hanyar da zasu iya rike iyalansu tare da samar wa masu kaddara mafita da cire masu fargaba yayin da suke son siya ko siyarwa, mun kasance kamar wasu garkuwa ga mai neman haya da kuma mai gida haka kuma mun kasance garkuwa ga mai kaddarar fili ko gida da kuma mai saya, saboda haka mun samu nasarar samar da kwanciyar hankali ga masu kaddarori.

To a yanzu wani matsala kungiyar taku take fuskanta a gida da waje?

Bamu da wani matsala face bukatar mu ga gwamnati a kan su kara bamu mahimmaci don magance rigingimu da ake samu nan da can, muna kuma fuskantar matsalar masu hurda wadanda basu yi ragista ba sai abu ya lallace lokacin ne za a zo wajenmu neman mafita, saboda haka ya kamata mutane su tabbatar sun a hurda ne da ‘yan kungiyar mu masu ragista.

Akwai wani ciniki da ka yi wanda ya burge ka a wannan sana’ar taku?

Akwai a kwanakin baya wani attajiri ya zo yana son zai sayi fili to sai ya zo wajena na zaba masa waje ya siya bisa jin dadin da ya yi ne ya bani damar in gina masa gidan in rike masa gidan bisa amana baya ga alherin daya bani tare da kulla zumunci mai karfi gaske don haka bazan manta da wannan ciniki a tarihi ba.

Wani kira za ka yi ga ‘yan kungiyar taku gida da waje?

Kira na ga ‘yan kungiyar mu gida da waje shi ne mu rike gaskiya domin gaskiya ne kashin bayan ci gaba ko wace sana’a wanda hakan ne ya sa muke samun ci gaba a yanzu haka sai bangaren masu bukatar sayan fili to in suna so su kubuta daga sharrin ‘yan 419 to in zasu saya ko sayarwa to su zo ga wakilanmu tare da lauyoyinmu mu basu shawara ta gari, idan mutum ya zo da bukatar sayan fili ko gida a tabbatar da an yi bicike a kan takardun daya gabatar saboda kauce wa cinikin da zai kai ga an fada rikici, in kuma an sami wani matsala a gaggauta sanar da mu shugabanin kungiya domin mu samar da hanyar warware matsalar.

 

What's Your Reaction?

Angry Angry
0
Angry
Cute Cute
0
Cute
Fail Fail
0
Fail
Geeky Geeky
0
Geeky
Lol Lol
0
Lol
Love Love
0
Love
OMG OMG
0
OMG
Win Win
0
Win
WTF WTF
0
WTF

Comments 0

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Riko Da Gaskiya Ne Sirrin Ci Gaban Sana’armu Na Sayar Da Gidaje -Sa’idu Sambawa

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format