Rikici ya barke gabanin zabuka a Turkiyya


Wata fastar shugaban Turkiyya a wani ganagamin yakin neman zabe a IstanbulHakkin mallakar hoto
AFP/GETTY

Image caption

Wata fastar shugaban Turkiyya a wani ganagamin yakin neman zabe a Istanbul

A kalla mutum uku ne su ka mutu yayin da takwas kuma su ka yi raunuka a wani ba takashi da makamai a garin Suruc da ke kudancin Turkiyya, kusa da iyakar Syria.

Suruc gari ne da ke da rinjayen Kurdawa. Rikicin ya barke ne a lokacin da wani dan majalisa Ibrahim Halil Tildiz dan jam’iyyar AK mai mulki kekamfe din sa na zabukan da za a gudanar kwanan nan.

Kafofin watsa labarai masu goyon bayan gwamnati sun ce wasu Kurdawa masu tsaron shaguna sun kai wa tawagarsa farmaki, amma majiyoyin bangaren adawa sun ce masu tsaron dan majalisar sun bude wuta.

A baya bayan nan ne wani hoton bidiyo ya bayyana, inda a ka nuna Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya na zuga jami’an jam’iyya da su tsorata Kurdawa domin samun kuri’u.Source link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *