Rike Hannu Na Kara Kaifin Kwakwalwa -BincikeLokacin da kake kokarin taimakawa wani masoyin ka wanda ke cikin wani mawuyacin hali, a irinwannan lokaci komai naka duk sun ta’allaka ne akan yadda shi wannan mutumin yake ciki. Wannan wani sabon hasashe ne wanda aka buga wannan mako da muke ciki wanda kuma an yi magana ne akan abubuwan da aka tattauna, a wata mujalla ta National Academy of science. (PNAS)

Shi wannan nazarin da aka yi kamar yadda masu binciken suka da suka fito daga jami’ar Colorado Boulder da kuma Jami’ar Haifa, suma sun gano cewar, da akwai yadda mutum ya kan ji ba dadi, kamar yadda shi ma abokin shi idan wani abu yana damun shi, manufa nan ita ce, duk suna gane cewar idan an samu sauki suna samun sako daga kwakwalwa.

‘’Mun bullo da hanyoyi da yawa wajen tuntuba da juna a duniyar zamani, ta haka kuma mun gano cewar akwai ‘yan takaitattun hanyoyi na ganawa da juna’’ a cewar shugaban marubuta Pabel Goldstein wanda wani mai bincike ne akan akan jin zafi, yana kuma karatu ne akan matsayin neman digirin digirgir.’’ Ita kasidar ta yi bayani ne akan karfi da kuma muhimmancin tabawa.

Shi nazari shi ne da dumi dumin shi a bangaren nazarin domin gano yadda’’ Yadda ake tuntubar juna tsakanin mutane’’ saboda ta hakan mutane suna ganin mutane yadda mutanen da suke tare da kuma alaka dasu a zuciya, wannan shi ne abu na farko da za’a duba a cikin kwakwalwa idan ana magana akan jin zafi, don haka ta bada wani sabon babi akan amfanin kwakwalwa zuwa kwakwalwa, da dai sauransu kamar tabawar da ke samar da samun sauki, ko kuma tabawar dake samar da sauki.

Sai Goldstein ya bullo da wata sabuwar hanya ta yin wani gwaji, lokacin da ake haihuwar ‘yarsa, sai ya gane cewar,lokacin da ya kama hannun mtar shi, sai ya lura ashe abin ya sa ta samu sauki.

‘’Ina son in gwada abin a dakin gwaji, shin ko gaskiya ne abin yana rage jin zafi bayan an taba, idan kuma haka ne to ta yaya’’?

Ya ce,shi abokan aikin shin a jami’ar Haifa sun samu mutane 22 maza da mata masu kuma shekarau daga 23 zuwa 32, wadanda suke tare har shekara daya, akakuma sa su, a wasu abubuwa na minti biyu, na farko suna zaune tare ne, amma ba a taba juna, da kuamwadanda suke zaune suna rike da hannuwan juna, suna kuma zauna ne a dakuna daban daban. Sai suka sake yin haka kamar yadda su matan aka sa suna jin zafi a hannuwansu.

Domin kasancewa tare ko dai da tabawa ko babu, ba za a rasa wani abu ba, wanda ya yi dangantaka da yadda kwakwalwa ke taka rawa wajen sadarwa, musamman yadda ake tsayar da hankali akan, alal misali, idan suka rike hannu lokacin da take jin zafi.

Masu binciken sun gano da cewar lokacin da take jin zafi bai kuma taba ba, sai kuma ba wani abin da kwakwalwa zata iya yi, wannan kuma ya yi dai dai da bayanan da aka samu, awata mujalla da aka buga, wannan ya nuna yadda bugun zuciya da kuma al’amuran numfashi suka kasance babu, lokacin da namijin bai kama hannunta ba, domin ya rage mata jin zafi.

‘’Wannan ya nuna ke nan jin zafin ya kawo matsala tuntuba tsakanin juna lokacin da tabawar ta dawo da wani samun sauki’’

Akwai wasu gwaje gwajen da aka yi da suka kuma nuna da zarar ya nuna kamar zafin da ta keji abin ya dame shi, lokacin ne kwakwalwa zata yi aiki, daga nan kuma sai jin zafin ya ragu.

Ta yaya kuma maganar tabawar zai iya zama taskar wani magani mai warkar da zafin ciwo?

 

What's Your Reaction?

Angry Angry
0
Angry
Cute Cute
0
Cute
Fail Fail
0
Fail
Geeky Geeky
0
Geeky
Lol Lol
0
Lol
Love Love
0
Love
OMG OMG
0
OMG
Win Win
0
Win
WTF WTF
0
WTF

Comments 0

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Rike Hannu Na Kara Kaifin Kwakwalwa -Bincike

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format