Nijeriya Na Kan Gaba Wajen Samar Da Kasuwa Ga Wayar Salula A Nahiyar AfrikaBabbar Shugaba ta kamfanin Jumia Nigeria, Juliet Anammah ta danganta Nijeriya a matsayin kasar dake kan gaba wajen samar da kasuwar sayar da wayar tafi da gidan ka kuma take bayar da dama wajen yin gasa a tsakanin kasashen da suke ci gaba.

Sai dai Juliet Anammah ta yi nuni da cewa, habakar tattalin arzikin Nijeriya bai da sauri indan aka kwanatn ta shi da sauran takwarorin ta, amma ana cike da fata da kuma cika alkawura.

A cewar Anammah, bunkasar wayar tafi da gidan ka da kamfanin Jumia Nigeria ya wallafa a  shekarar 2017 ya nuna cewar Nijeriya tana a kan gaba wajen samar da kasuwa ta sayar da wayar tafi da gidan ka a fadin nahiyar Affrika wanda kuma akayi ammana da hakan.

Rahoton a takaice ya yi fashin baki akan yadda ake yin amfani da kafar internet, inda hakan ya sanya aka kara samu mutane suna komawa yin amfani da wayar tafi da gidan ka kirar (smartphone) da kuma rawar da masu ruwa da tsaki suke takawa a harkar.

Bugu da kari, Kamfanin na Jumia Nigeria a shirye yake wajen sakin sabon rahoton akan wayar tafi da gidan ka a shekarar 2018.

Wannan kudurin zai mayar da hankali ne akan sababbin hanyoyi na wayar tafi da gidan ka Nijeriya da kuma nahiyar Afrika baki daya.

Anammah ta bayyana cewar, ta ji dadi matuka fiye da kowa akan wannan rahoton, ta kuma kara da cewa, daga  ranar sha biya zuwa ashirin da biyarr na watan Maris na shekarar 2018, zai yi kyau da kuma nuna jin dadi ga kasar nan a bisa dalilai guda biyu, inda tace, a shekarar 2018 za a fitar da rahoto karo na hudu akan yadda ake yin amfani da wayar tafi gidan a Nijeriya a lokacin taron manema labarai na biyu kuma, koda yake wanda shima har yanzu yana da danganta ka da taron na farko shine yadda Kamfanin na Jumia fara yin Jumia zai gudanar taron sati na akan sayar da wayar tafi da gidan ka akan farashin da ya dace a kasar nan.

 

What's Your Reaction?

Angry Angry
0
Angry
Cute Cute
0
Cute
Fail Fail
0
Fail
Geeky Geeky
0
Geeky
Lol Lol
0
Lol
Love Love
0
Love
OMG OMG
0
OMG
Win Win
0
Win
WTF WTF
0
WTF

Comments 0

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Nijeriya Na Kan Gaba Wajen Samar Da Kasuwa Ga Wayar Salula A Nahiyar Afrika

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format