Nasarar Ronaldo ta harzuka wasu magoya bayan Man Utd


Sau uku Ronaldo ya dauki kofin gasar firimiya a Old TraffordHakkin mallakar hoto
PA

Image caption

Sau uku Ronaldo ya dauki kofin gasar firimiya a Old Trafford

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United sun zabi Cristiano Ronaldo a matsayin dan wasan ya fi taka rawa a tarihin kungiyar a gasar Firimiya.

Sai dai kuma al’amarin ya harzuka wasu magoyan bayan kulob din, wadanda suke ganin zabin bai dace ba.

Machester United ce ta nemi magoya bayanta su kada kuri’a kan rukuni hudu da ta ware kafin ta buga wasanta na 1000 a Firimiya a karawar karshen gasar bana da ta yi da Watford.

An tambayi magoyan bayan Manchester a kan wanda ya fi zira kwallo mafi kyau a raga, da hana kwallo shiga raga mafi tsauri, da wasan da ya fi birge su tun bayan watan Agusta na shekarar 1992.

Sai dai babu wata jayayya a rukunin uku na farko inda aka zabi Wayne Rooney saboda kwallon da ya zura a wasan da suka doke Manchester City 4-3 a 2009. An kuma zabi wasan a matsayin wanda ya fi kayatar da magoya bayana kungiyar.

Hana kwallo shiga raga da David de Gea ya yi wanda Juan Mata ya buga a shekarar 2012 ya kasance shi ne wanda magoya bayan kungiyar suka fi so.

Sai dai an rika ce-ce ku-ce game da sakamakon da aka fitar a kan Ronaldo, inda magoya baya da dama ke ganin cewa akwai ‘yan wasa da suka fi taka rawa fiye da shi.

Ronaldo ne ya zo na farko, Ryan Giggs ya zo na biyu yayin da Paul Scholes ya zo na uku.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wasu kuma sun nuna damuwa kan yadda aka watsi da Eric Cantona a zaben

Wasu magoyan bayan United sun bayyanna ra’ayoyinsu a Twitter inda suka ce akwai alamar tambaya game da sakamakon, inda wasu suka ce ya kamata a dubi yawan kofin da Giggs da Scholes suka dauka a Firimiya kuma a kwatanta su da yawan kofin da Cristiano Ronaldo ya dauka.

Wasu kuma na ganin rawar da Eric Cantona ya taka ta fi ta Ronaldo wanda ya yi shekara shida yana taka leda a kungiyar daga shekarar 2003 zuwa 2009.

Amma kuma idan ana son yi wa dan wasan na Real Madrid adalci, sau uku ya dauki kofin Firimiya, kuma a 2008 ya lashe kyautar Balon d’Or da kuma gwarzon dan wasan kwallon kafa na FIFA a Manchester United.

Kuma Ronaldo ya zamo dan kwallon da ya fi kowa zura kwallo a gasar a kakar 2007-08.Source link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *