Mutum 38 sun mutu a hatsarin mota a HabashaMap of Ethiopia

Jami’ai sun ce mutum 38 ne suka mutu a Habasha bayan da motar bas da suke yin buolaguro a ciki ta rufto daga kan wata gasa.

Hatsarin ya faru ne a gundumar Amhara da ke arewacin Addis Ababa babban birnin kasar.

Jami’ai a yankin sun tabbatar da mutuwar maza 28 da mata 10.

Kafar yada labaran Fana ta ruwaito cewar fasinjoji 10 ne suka rayu amma sun ji munanan raunuka.

Ta kara da cewa mafi yawan wadanda hatsarin ya rutsa da su daliban jami’a ne.

Wata kafar yada labarai mai zaman kanta ta kasar Addis Standard, ta ce motar ta fado ne daga nisan mita biyar.

Kasar Habasha dai wadda tana daya daga cikin kasashen Afirka da tattalin arzikinsu ke habaka, ta fadada da kuma gyara titunanta a shekarun baya-bayan nan.

Mutane da dama sun fi amfani da motocin bas na safa don yin doguwar tafiya.

What's Your Reaction?

Angry Angry
0
Angry
Cute Cute
0
Cute
Fail Fail
0
Fail
Geeky Geeky
0
Geeky
Lol Lol
0
Lol
Love Love
0
Love
OMG OMG
0
OMG
Win Win
0
Win
WTF WTF
0
WTF

Comments 0

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Mutum 38 sun mutu a hatsarin mota a Habasha

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format