Mufti Menk ya yaba da saukin kan Dangote


Shahararren malamin addinin Islama na kasar Zimbabuwe, Isma’il Ibn Musa Menk, wanda aka fi sani da Mufti Menk ya zo Najeriya dan gabatar da wata muhadara data shafi addini, ya hadu da attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote inda ya yaba da saukin kanshi duk da Allah ya bashi Duniya.

Yace mutane masu saukin kai duk da cewa sun samu abinda wasu da dama basu samu ba sukan birgeshi, daga daga cikin irin wadannan mutane shine Aliko Dangote na Najeriya, dan uwane dake taimakawa miliyoyin jama’a, shi yafi kowa kudi a Afrika, Ina fatan Allah ya kara mishi Albarka.Source link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *