Masari Da Bugaje Za Su Jagoranci Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya Na BanaGwamnan jihar Katsina, Rt. Hon. Bello Masari da tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa a zamanin tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, wato Dr. Usman Bugaje ne za su jagoranci taron Marubuta Hausa Ta Duniya wanda a za a gudanar a birnin Katsina ranar Juma’a 16 zuwa Lahadi 18 ga Maris, 2018.

Kunshin bayanin hakan ya fito ne a cikin takardar gayyatar taron, wacce shugaban babban kwamitin taron na bana, Malam Rabiu Na’auwa, ya sahalewa.

A cikin katin gayyatar an nuna cewa, gwamnan na jihar ta Katsina shi ne babban bako na musamman, yayin Dr. Bugaje zai kasance shugaban taron na bana. Sarakunan Katsina da Daura, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman da Alhaji Umar Faruk, su ne kuma iyayen taron.

Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Malam Ibrahim Wakkala, ne zai kasance babban bako na musamman, yayiin da babban bako mai jawabi a wajen taron kuwa shi ne Farfesa Ibrahim Malumfashi na jami’ar jihar Kaduna.

Haka zalika, gwamnatin jihar Katsina ce mai masaukin baki a wannan babban taro na marubuta Hausa na duniya. Wata majiya ta kara ma na da cewa, fitaccen marubuci kuma dan jarida, Malam Danjuma Katsina, zai bayar da masauki ga baki mata a wani gidansa saukar bakinsa da ke cikin garin Katsina.

Za a gudanar da wannan gagarumin taro a karo na biyu ne a dakin taro na hukumar kula da kananan hukumomin jihar ta Katsina da ke kan titin Kaita daura da Majalisar Dokokin jihar. Kuma za a rika bude taron ne da misalin karfe 9:00 na safe.

Idan dai za a iya tunawa, an gudanar da taron karo na farko ne a birnin Kano cikin shekara ta 2016 a karkashin jagorancin fitaccen marubucin nan, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON.

Shugaban Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya na bana, wato Alhaji Usman Bugaje, ya na da digirin digirgir ne a fannin ilimin tarihi.

 

What's Your Reaction?

Angry Angry
0
Angry
Cute Cute
0
Cute
Fail Fail
0
Fail
Geeky Geeky
0
Geeky
Lol Lol
0
Lol
Love Love
0
Love
OMG OMG
0
OMG
Win Win
0
Win
WTF WTF
0
WTF

Comments 0

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Masari Da Bugaje Za Su Jagoranci Taron Ranar Marubuta Hausa Ta Duniya Na Bana

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format