Masana’antun Wutar Lantarki Ke Shirya Wa Gwamnati Makarkashiya –FASHOLAMinistan Ma’aikatar Wuta da Ayyuka da Gidaje Babatunde Raji Fashola, ya yi zargin cewar masana’antun dake samar da wutar lantaki a kasar nan suna shirin rikita samar da wutura lantarki a daukacin fadin kasar nan da nufin gogawa Gwamnatin Tarayya kashin Kaji.

Fashola ya furta hakan ne a martanin da ya mayar akan rahitannin da wasu masana’antun da suka maka gwamnatin tarayya a koto.

Ministan wanda ya furta hakan a ranar Litinin data gabata yace,”wannan yunkurin nasu yana kan doka, amma su sani cewar su zama a cikin shiri domin kuwa Kotun zata kwance masu zani ne a kasuwa idan aka yi la’akari da ra’ayoyin alummar gari.”

A makon da ya gabata majiyar mu ta ruwaito cewar, wasu masana’antun sun maka gwamnatin tarayya a gaban babbar Kotun dake Abuja a bisa zargin nuna masu ban-banci akan ra’ayoyin su da kuma masu samar da iskar Gas.

Har ila yau, Masana’antun sun zargi gwamnatin tarayya akan bai wa kamfanin samar da wutar lantarki na Azura West Africa da kuma kamfanin Accugas fifiko akan sauran kamfanonin samar da wutar.

Amma da yake jawabi a taro karo na ashirin da biyar na wata-wata akan masana’antar samar da wutar lantarki a garin Uyo Minista Fashola yace masana’antun dole ne su zama a shirye wajen yiwa masu yin amfani da wutar lantarki bayani duk da cewar sun amfana daga gwamnatin tarayya kuma suna shirin yiwa gwamnatin zagon kasa ta hanyar kin samar da wuta ga ‘yan kasa.

Fashola ya ci gaba da cewa,“barin in shedawa masu samar da wutar cewar na samu rahotanni akan tarurrukan da suka yi a asirce cewar wasu daga cikin su suna yunkurin dakatar da samar da wuta a bisa nufin su na siyasa.”

Acewar sa,”ina baku shawara cewar wadanda suka san cewar da gaske a shirye suke don suyi kasuwanci, gwamnati a shirye take ta basu dukkan goyon bayan da ya dace da kuma yin hadaka dasu.”

Ya kara da cewa, amma ga wadanda suka shiga kasuwancin ba tare da fahimta ba, ya kamata su tashi tsaye suyi aiki tukuru don su taimaka mana wajen sake ciyar da kasar nan gaba.”

Ministan ya yi nuni da cewa, “wadanda suka zabi fakewa da Kotu na wucin gadi suna iya yin hakan, amma su sani cewar, Kotun zata kwance masu zani ne a kasuwa kawai.”

Fashola ya bayyana cewar,“na fadi hakan ne domin wata kilan don kusani cewar a yanzu ‘yan Nijeriya suna daukar makomar su ce a hannun su kuma wannan shine dalilin da yasa aka sayar da hannun jarin kadarorin gwamnati.”

Acewar Fashola idan kunyi dubi zaku ga cewar wasu ‘yan Nijeriya tuni sun fara yin amfani na na’urorin samar da wuta mai aiki da hasken rana da suka kakkafa akan shigifar gidajen su kuma karamin layin samar da wutar lantarki na kasa ya basu damar yin amfani da megawatt daya ba tare da lasisi ba.”

Fashola ya kara yin nuni da cewa,“ wannan hanyar har tafi girma akan yadda aka saba samar da wutar lantarki kuma babu wata doka data bai wa masana’antun damar daukewa wuta baki daya ga yan kasar nan.”

Acewar sa,”banajin tsoron Kotu kuma zamu hadu daku a can don mu kare matsayin mu, amma dai na san cewar dole ne masana’antun su zamo a cikin shiri don su san ra’ayin kotu, inda ya yi nuni da cewa Kotu tana yin amfani ne da hankalin ta.”

Fashola ya bayyana cewar, masana’antu su kuma zamo a cikin shiri wajen yiwa ‘yan kasa bayani akan ya ya ta kwaranye da wasu gungun ‘yan kasa nan masu amfani da wutar lantarki suka shigar da kara a gaban Kotu akan dakatar da kaddamar da karin kudin wuta da hukumar dake sanya ido akan samar da wuta taso ta yi a shekarar 2016.

Ministan ya kara da cewa, masana’antun su kuma zama a cikin shiri wajen yiwa Kotun bayani akan ko sun kai karar ce kafin gwamnati ta amince da biyan naira 701 Inshora wajen biyan bil din kudin wuta na wata-wata.

Acewar sa,“dole kuma su fadawa kotun cewar ana binsu basussuka tun kafin gwamnatin Shugaba Buhari ta dare karagar mulki domin kudin shigar su ya ragu da kashi hamsin bisa dari.”

Har ila yau, Fashola yace, dole ne kuma su shedawa Kotun cewar a yanzu sun karbi kimanin kashi tamanin bisa dari na kudin shigar su kuma a yanzu wannan gwamnatin tana basu kudin haraji daga masu amfani da wutar dake kasar waje da suka hadada kasashen Benin da Nijer da Togo kuma suna karbar kudin akan dalar Amurka, ba kamar yadda ake biyan su da naira ba.

Ya kara da cewa, “dole ne kuma su shedawa Kotun cewar sun kawo karar ce saboda gwamnati zata kara biyan sababbin masana’antu kudi kashi dari bisa dari wanda yasha ban-ban da ka’idar yarjejeniyar da aka kulla da sababbin masana’antun wanda su basu dashi.

Fashola yace, haka kuma dole su shedawa Kotun cewar sun gudanar da taro da gwamnatin sun kuma gabatar da bukatun su wanda kuma gwamnatin ta yi alkawarin yin dubi akan bukatun a cikin mako daya kafin su maka gwamnatin a Kotu.

What's Your Reaction?

Angry Angry
0
Angry
Cute Cute
0
Cute
Fail Fail
0
Fail
Geeky Geeky
0
Geeky
Lol Lol
0
Lol
Love Love
0
Love
OMG OMG
0
OMG
Win Win
0
Win
WTF WTF
0
WTF

Comments 0

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Masana’antun Wutar Lantarki Ke Shirya Wa Gwamnati Makarkashiya –FASHOLA

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format