Mai jego na shirin kafa tarihi a gasar Tennis


A ranar Asabar mai zuwa ne Serena da ke jego, za ta fafata da Angelique Kerber ‘yar kasar Jamus a wasan karshe, watanni 10 kacal bayan haihuwa da ta yi a watan Satumba na shekarar 2017.

Idan Serena ta samu wannan nasara za ta zama mai jego ta farko da ta lashe kofi a daya daga cikin manyan wasannin kwallon tennis cikin shekaru 38, bayan tarihin da Evonne Googlagong ta kafa.

A shekarar 1980 Evonne Googlagong ‘yar kasar Australia, ta kafa tarihin zama mai jego ta farko da ta lashe kofin babbar gasar Tennis a duniya.

rfihausa.Source link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *