Magoya Bayan Mu Suna Son Mu Lashe Firimiya A Wasan Da Za Mu Kara Da Manchester United, Inji GuardiolaMai koyar da yan wasan kungiyar Manchester City, Pep Guardiola,  yace Magoya bayan  kungiyar  suna son su lashe kofin firimiya a wasan da zasu kara da Manchester United a filin wasa na Ettihad dake birnin Manchester

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City na dab da lashe kofin gasar firimiya na Ingila a bana, bayan ta samu nasarar casa Stoke City da kwallaye 2-0 a karawar da sukayi a ranar Litinin.

Dan wasa Dabid Silba ne ya ci wa Manchester City dukkanin kwallayenta biyu a minti na 10 da kuma na 50 da wasan bayan ya murmure daga raunin dayaji a satin daya gabata.

Yanzu haka Manchester City ta bai wa Manchester United da ke bin ta tazarar maki 16 a teburin gasar ta firimiya duk da cewa a cikin wata mai zuwa kungiyoyin biyu da ke hamayya da juna za su barje gumi a filin wasa na Etihad.

Ko da dai Manchester City za ta fara fafatawa ne da Eberton kuma tana bukatar samun nasara akan ta kafin kara samun kwarin gwiwar lashe kofin a bana.

Matukar dai ta daga kofin, to zai kasance a karon farko kenan da Manchester City ke lashe gasar ta firimiya a karkashin kocinta, Pep Guardiola.

What's Your Reaction?

Angry Angry
0
Angry
Cute Cute
0
Cute
Fail Fail
0
Fail
Geeky Geeky
0
Geeky
Lol Lol
0
Lol
Love Love
0
Love
OMG OMG
0
OMG
Win Win
0
Win
WTF WTF
0
WTF

Comments 0

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Magoya Bayan Mu Suna Son Mu Lashe Firimiya A Wasan Da Za Mu Kara Da Manchester United, Inji Guardiola

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format