Maganin Zazzabin Lassa Kyauta Ne, Inji Gwamnatin Nijeriya Sashin Kimiyya Da Fasaha Zai Samu Tallafi Naira Biliyan 12.2Da zaran kanfanin MDDi ta bayar da Naira Biliyan 2.5 da ta sanar kwanan nan ga sashin sadarwar kimiyya da fasaha na Intanet a kasar nan, kudaden da ke a sahsen zai kai Naira Biliyan 12.2 ke nan.

Kanfanin na MDDi ya dai sanar da shirin ta na zuba jarin Naira Biliyan 2.5 domin karfafa harkokin ta a Nijeriya  abin daya kai jarinta a wannan shashin daga Naira Biliyan 10.7 a zango na farko zuwa Naira Biliyan 12.2 a wannan zangon na biyu. Wannan jarin ta aka zuba zai karfafa aikin kanfanin na samar da guraben intanet a kasar nan daga 300 zuwa 600.

Shugaban kanfanin MDDi, Mista Gbenga Adegbiji, ne ya bayyana haka, ya kuma kara da cewa, “Bukatar masu hurda damu ne yake kara mana kaimin fadada aikin da muke yi, a halin yanzu an mallake gurabe 300 da muka samar a shekara 2015 a cibiyar mu ta Lekki a Legas”

Adegbiji ya ce, tun da aka bude kanfanin MDDi a shekarar 2015 an kashe Dala Miliyan 35 kwatankwacin Naira Biliyan N10.7 wajen samar da kayan aiki na zamani a cikin shekara 5 da ya gabata.

Adegbiji ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya in da ya ce, “Lokaci ya yi da gwamnatin tarayya za ta samar da tsare-tsare da zai tilastawa kanfanoni masu zaman kansu da hukumomin gwamnati su kafa kafafen urabe sadarwa na intanet a ma’aikatunsu domin bunkasar tatalin arziki da dalilai na samar da tsaro”

“Dole gwamnatin tarayya ta sani cewa, samar da cibiyoyin sadarwa daga cikin kasa yana da mahimmancin gaske saboda in har daga kasashen waje ake kafa wa kanfanoni da hukumomin mu cibiyar intanet, haka na nuna kenan sai kasashen waje sun ga abin da aka aiko kafin mu a nan gida mu iya gani ke nan, abin kuma da zai iya sa harkar tsaron kasa cikin hatsari.”

“Fiye da kashi 70 na bankuna a Nijeriya na amfani da intanet da MDDi ke samar wa 21 daga cikin su suna da wani hurda intanet ko dan ya ya da MDDi, fadadawar da muka samu daga gurbi 300 zuwa gurbi 600 ya farunne saboda tsananin bukatar da ke fitowa daga abokan hurdanmu”inji shi.

“A watan Maris za a karar da tanadin da muke da shi hakan ya sa muke ta kokarin samar da karin gurabe 300, a halin yanzu ma wasu kanfanoni sun riga sun nuna bukatar sun a gurabe intanet da zamu samar a zango na gaba”

Ya kuma amince da maganar da ke yi na cewa, harkar samar da guraben intanet yana da tsananin bukatar kudade masu dinbin yawa saboda haka ya bukaci gwamnatin tarayya ta kawo wa harkar samar da intanet agaji don bunkasa harkar a Nijeriya”

“A kwai bukatar sa ido a tafiyar da harkokin samar da intanet a kasar nan, ya kamata gwamnatin tarayya ta aiyana cibiyoyin samar da intanet a matsayin cibiyoyi masu mahimmanci ga kasa saboda gudumawarsu ga tattalin arzikin kowanne kasa”

Da yake kara haske a kan aiyukan MDDi a Nijeriya, Mista Adegbiji ya ce, “Kanfanin MDDi ne ya fi kownne girma a yankin Afrika ta yamma da ke gabatar da cikkaken harkokin da suka shafi samar wa da rarraba intanet da sauran harkokin da suka shafi intanet a yankin Afrika ta Yamma” Kanfanin MDDi ne kan gaba da ke gabatar da aiyukansa a Legas da Sagamu da Accra da kasar Code D’Iboire da kuma Senegal”

Adegbiji ya kara da cewa, kanfanin MDDi na da tsari da gogewa irin na takwarorinsa a ko’ina a duniya, an yi mata gini mai tsarin TIA 942 tare da mataki na “Tier III Standards” da kuma “West Africa’s Tier III” tare da shaidawar PCI DSS da ISO 27001da kuma 9001.

Masu hurda da kanfanin MDDi na iya hurda kai tsaye da masu irin wannan hurdar a yanki Afrika ta Yamma, za kuma su iya musayan bayanai da takwarorinsu a kasashen Ghana da Amsterdam da kuma Landan.

Da yake jaddada bukatar da ake da shi na gwanatin tarayya ta kawo wa sashin agajin gaggawa, ya ce, “Kashi 60 na abubuwan da ake bukata a sahashin shi ne wutan lantarki, saboda tsananin  bukatarmu na wutar lantarki da kuma matsalar wutan lantarki a kasar nan, hakan yana kuma kara kudin harkar samar da intanet a kasar nan”

Ya kuma kara da cewa, “Ya kamata gwamnatin tarayyar Nijeriya ta tilasata wa kanfanoni da hukumomin gwamnati dasu rinka hurda da kanfanin samar da intanet a cikin gida saboda samar da intanet a cikin gida zai saukar da tsadar kudin da ake samu a wajen kafa intanet a kasar nan” ya kuma kara da cewa, lallai wasu hukumomin gwamnati na hurda da kanfanin MDDi amma ana da bukatar karin hukumomin gwamanti su rinka hurda da MDDi saboda har yanzu wasu hukumomin na hurda da kanfanonin samar da intanet na kasashen waje.

Ya ce, Nijeriya na tsananin bukatar masu zuba jari mai yawa a fagen samar da intanet saboda fadada yawan masu amfani da intanet a kasar nan. “Yawan masu hurda da intanet da ake dasu zai kara kwarewar kanfanonin mu hakan kuma zai kara rage tsadar da ake fama da shi a kasar nan”

Daga nan ya kuma kara da cewa, kanfanin MDDi ita ce kadai a kasar nan ke samar da tsarin sadarwa na OTTs a Nijeriya, ita ce kuma kadai da ke da hanyar sadarwa a cikin ruwa har na tsawon kilomita 10 a cikin teku mai nau’in ACE da WACS da Glo 1 da kuma MainOne. Cibiyar samar da intanet din na kuma da zurfin Kilomita 20 na “Primary and secondary data centre” domin isar da sako ga ko ina a duniya.

What's Your Reaction?

Angry Angry
0
Angry
Cute Cute
0
Cute
Fail Fail
0
Fail
Geeky Geeky
0
Geeky
Lol Lol
0
Lol
Love Love
0
Love
OMG OMG
0
OMG
Win Win
0
Win
WTF WTF
0
WTF

Comments 0

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Maganin Zazzabin Lassa Kyauta Ne, Inji Gwamnatin Nijeriya Sashin Kimiyya Da Fasaha Zai Samu Tallafi Naira Biliyan 12.2

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format