Kwamitin Gina Jami’ar Jihar Zamfara Ya Mika Rahotansa Ga Gwamna Yari Gwamna Yari Ya Ba Sarkin Birnin Magaji Takardar Kama AikiGwamna Abdua’ziz Yari ya ba Sarkin Birnin Magaji watau Dan Alin Birnin magaji na Sha hudu takardar kama aikin a dakin taron gidan gwamnati da ke Gusau, babban birnin jiha Zamfara. Gwamna Yari ya bayyana da ta’aziyar marigayi Dan Alin Birnin Magaji na Sha uku Alhaji Ahmad Umar Usman da rasuwa ce wace ta girgiza al’umma, “muna fatan Allah ya jikansa da Rahama. Kuma a yau za mu ba wanda Allah ya maye makwafinsa, Alhaji Hussaini Maude Usman a matsayin magajinsa. Kuma wannan magaji nasa muna fatan zai kokari ya kamanta sadaukarwarsa ga al’ummar Karamar Hukumar Birnin Magaji da jihar Zamfara da Kasa baki daya. Kuma wannan takardar kama aiki ta zamo maka jogon hada kan masarauta da kuma cigaban al’ummarka.

Shi ne Alhaji  Dan Kulu dan Masanin Birnin Magaji ya jinjina wa majalisa Masarauta a kan gani cancantar , Mai martaba Alhaji Hussaini Usman.a matsayin magajin marigayi, Alhaji Ahmad Umar.da kuma godiya ga Gwamna Abdua’ziz Yari da ya tabbatar da shi Dan Alin Birnin magaji na Sha hudu kuma ya ba shi takardar kama aiki nan take. Da fatan duk Wanda ya halarci wannan bikin Allah ya mai da shi gida lafiya, Amin.

What's Your Reaction?

Angry Angry
0
Angry
Cute Cute
0
Cute
Fail Fail
0
Fail
Geeky Geeky
0
Geeky
Lol Lol
0
Lol
Love Love
0
Love
OMG OMG
0
OMG
Win Win
0
Win
WTF WTF
0
WTF

Comments 0

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Kwamitin Gina Jami’ar Jihar Zamfara Ya Mika Rahotansa Ga Gwamna Yari Gwamna Yari Ya Ba Sarkin Birnin Magaji Takardar Kama Aiki

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format