Jamus: Merkel ta fara wa'adi karo na hudu a matsayin shugabar gwamnatiMerkel mai ra’ayin mazan jiya za ta jagoranci babbar gwamnatin kawance da jam’iyyar SPD, sai dai tazarar kuri’un ba yawa, wato kuri’u tara ne kacal.

A zagayen farko na zaben, wakilai 364 na majalisar suka kada kuri’ar amincewa yayin da 315 suka nuna rashin amincewa. Bayan zaben da kuma rantsuwar kama aiki da ta sha a majalisar dokokin, an ayyana Merkel a matsayin shugabar gwamnari a fadar Bellevue ta shugaban kasa Frank-Walter Steinmeier.

Bangaren gwamnatin kawancen tsakanin hadin gwiwar jam’iyyun CDU-CSU da kuma SPD yana da kujeru 399 a majalisar dokoki.

A wannan Larabar ce kuma za a ratsar da ministocin gwamnatin kawancen a majalisa kafin daga baya sabuwar majalisar ministoci ta yi zamanta na farko.

Kama aikin gwamnatin ya zo kusan watanni shida bayan an gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki, lamarin da ke zama irinsa mafi dadewa a tarihin tarayyar Jamus.

What's Your Reaction?

Angry Angry
0
Angry
Cute Cute
0
Cute
Fail Fail
0
Fail
Geeky Geeky
0
Geeky
Lol Lol
0
Lol
Love Love
0
Love
OMG OMG
0
OMG
Win Win
0
Win
WTF WTF
0
WTF

Comments 0

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Jamus: Merkel ta fara wa'adi karo na hudu a matsayin shugabar gwamnati

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format