Jadawalin Zabe: Majalisa Ta Ja Hankali INECMajalisar Datawwa ta gargadi Hukumar zabe ta kasa, INEC, kan raina karfin Majalisar a gyaran da Majalisar ta yi wa dokar zabe ta shekarar 2010.

Shugaban Majalisar ta Dattawa, Sanata Bukola Saraki ne ya yi wannan jan kunnen, a lokacin da yake bude zaman majalisar don tattaunawa a kan dokar da ta shafi aikata laifukan zabe ranar Litinin, inda ya yi nu ni da cece-kucen da aka yi ta yi a kan gyaran da Majalisar ta yi wa sashe na 25 na dokar zaben kwanan nan, wanda ya sake fasalin yanda za a gudanar da zaben a lokutan zaben.

A baya, hukumar zaben ta yi kurarin kai maganar gaban Kotu, kafin daga bisani kuma ta janye hakan.

Saraki, ya tabbatarwa da hukumar zaben cewa, Majalisar ta Dattawa tana da karfin ikon da za ta yi gyara a kan hukumar zaben da ma dukkanin sauran hukumomin gwamnati.

Saraki, wanda mataimakin Shugaban marasa rinjayen Majalisar, Bala Ibn Na’Allah, ya wakilce shi, ya yi nu ni da cewa, ‘Yan majalisun ba za su sanya kansu a kan kafa wata doka da ta sabawa tsarin mulki ba.

“Kwanan nan, ake ta yin ja in-ja, a kan ko wane ne ke da ikon yin hakan,” ya kara da cewa, akwai mutane da yawa a Nijeriya da suka san hanyar zuwa Kotu domin su sami duk wani hukuncin da suke so.

“Ya kamata INEC, ta yi taka-tsan-tsan, a kan ko wa take sauraro. Ba zai yiwu mu zauna muna kallon ana sabawa tsarin mulki ba. Ya kamata mu ja hankulan kanmu. Muna da bukatar wannan kasar,“ in ji Saraki.

Shugaban Majalisar Dattawan, ya kuma koka a kan yadda wasu ‘yan takara a wasu Jam’iyyun suke ta ayyukan kamfen, tun kafin hukumar zaben ta bayar da daman hakan.

Saraki, sai ya bukaci hukumar zaben da ta yi amfani da ikon ta wajen hana iren wadannan mutanan ko Jam’iyyun yin takara.

Shugaban Hukumar zaben ta kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, a na shi jawabin, ya bayyana cewa, a yanzun haka hukumar zaben tana fama da shari,u 1,080 a Kotuna da suka shafi zaben shekarar 2015.

Ya kara da cewa, hukumar zaben ta karbi tuhumomin karya dokar zabe guda 124 daga ‘yan sanda, kuma tuni ta hukunta guda 60 daga cikin su.

Yakubu, ya bayyana farin cikinsa da kafa hukumar ta kula da aikata laifukan zabe, ya bayyana cewa, INEC, ba za ta iya hukunta masu aikata laifukan zaben ba kai tsaye, ta mayar da hankalinta ne a kan dimbin ayyukan da ke gabanta.

Ayyukan da ke gaban hukumar zaben sun hada da, yin rajista da kuma daidaita kungiyoyin siyasa da kuma lura da su a wajen tarukan su da kuma yanda suke kashe kudaden su.

Sai dai kuma, shugaban hukumar zaben ya yi nu ni da cewa, kamata ya yi hukumar zaben ta nada Sakataren hukumar lura da aikata laifukan zaben da kan ta, ba wai Shugaban kasa ne ya kamata ya nada shi ba, kamar yanda ake bayar da shawarin hakan.

What's Your Reaction?

Angry Angry
0
Angry
Cute Cute
0
Cute
Fail Fail
0
Fail
Geeky Geeky
0
Geeky
Lol Lol
0
Lol
Love Love
0
Love
OMG OMG
0
OMG
Win Win
0
Win
WTF WTF
0
WTF

Comments 0

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Jadawalin Zabe: Majalisa Ta Ja Hankali INEC

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format