Gwamnatin Birtaniya ta kori wasu jami'an diplomasiyyar Rasha daga kasarA matsayin martani dangane da harin sinadari mai guba a yankin Salisbury da ake zargin Rasha da kai wa wani tsohon jami’in diplomasiyyarta, gwamnatin Birtaniya ta kori jami’an diplomasiyyar Rasha su 23 daga kasar. Bugu da karin gwamnatin ta Birtaniya karkashin jagorancin Firaminista Theresa May ta ce ba za ta tura wakilan gwamnati da na gidan sarauta zuwa gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da Rasha za ta dauki nauyinshi nan da wasu watanni masu zuwa ba.

A lokacin da take magana gaban majalisar dokoki a birnin London May cewa ta yi.

“Za mu dakatar da dukkan huldodi na tuntubar juna tsakanin manyan jami’an Birtaniya da Rasha, ciki har da janye goron gayyatar da muka ba wa ministan harkokin waje Lavrov na ziyartar Birtaniya. Muna kuma tabbatar da cewa ba bu wani minista ko wani dan gidan sarautar Ingila da zai halarci gasar cin kofin duniya na lokacin bazara a Rasha.”

Birtaniya dai na zargin Rasha da amfani da guba kan tsohon jami’in leken asirinta Sergey Skripal da ‘yarsa a Birtaniya, inda kuma ta nemi Rasha ta yi bayani, amma Rasha ta ce ba ta samu wata bukatar yin haka a hukumance ba.

What's Your Reaction?

Angry Angry
0
Angry
Cute Cute
0
Cute
Fail Fail
0
Fail
Geeky Geeky
0
Geeky
Lol Lol
0
Lol
Love Love
0
Love
OMG OMG
0
OMG
Win Win
0
Win
WTF WTF
0
WTF

Comments 0

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Gwamnatin Birtaniya ta kori wasu jami'an diplomasiyyar Rasha daga kasar

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format