Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna da matarshi sun kai ziyara gidan marayu


Elrufai da matarsa Ummi sun kai ziyarar ta’aziyya Gidan marayu tare da basu tabbacin 

Gwamnati ba zata bari su jigata ba. A yau Alhamis mai dakin Gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Aisha Ummi Garba El-Rufai tare da mai gidanta Gwamnan Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai suka kai ziyarar ta’aziyya gidan marayu dake Nasarawan Kaduna.

Gwamnan da matarsa sunje gidan marayun ne domin jajantawa marayun bisa rasuwar babbar mai kula dasu, Hajiya Hauwa Salis (uwar marayu) wacce Allah Ya yiwa rasuwa a daren ranar Litinin da ta gabata.

Kafin rasuwarta Margayiyar ta kasance itace wacce ta assasa gidan marayun kuma take kula dasu. A yayin ziyarar tasu a yau Gwamna El-Rufai ya umurci Kwamishiniyar kula da harkokin mata ta jihar Kaduna da ta dauki ragamar gidan marayun kuma tayi dukkan abunda ya dace domin ganin gidan bai ruguje ba. A gefe daya kuma mai dakin Gwamnan jihar Kaduna Hajiya Aisha Ummi El-Rufai ta kuduri aniyar rike gidan da sanya ido domin ganin yara marayun da aka bari su fiye da 170 basu tagayyara ba.

A karshe matar Gwamnan ta lashi takobin cigaba da ziyartar gidan marayun akai-akai har zuwa lokacinda Gwamnatin jihar zata kammala  tsara yadda gidan zai kasance. Hajiya Ummi da maigidanta El-Rufai sun jajantawa marayun da iyalan mamaciyar tare da yin addu’ar Allah ya jikan margayiya Hauwa.

Dama dai kafin rasuwar mamaciyar, Hajiya Aisha Ummi El-Rufai takan baiwa gidan marayun kyautar Shanu da kudaden cefene musamman a lokutan sallah.

Mashkur Ibrahim

(Mai taimakawa Matar Gwamnan a fannin duka ayyuka) 14/06/2018Source link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *