An rufe wuraren shakatawa a Kaduna


Gwamnatin Kaduna ta bayar da umurnin rufe dukkanin wuraren shakatawa da wasan yara a tsawon lokacin bukukuwan Sallah a jihar.

Hukumomin jahar cikin wata sanarwa sun bayyana fargabar tsaro a matsayin dalilin daukar matakin.

Kanal Yusuf Yakubu mai bai wa gwamnan Kaduna shawara kan sha’anin tsaro ya shaidawa BBC cewa tsoron fitina ne ya sa suka dauki matakin rufe wuraren shakatawar.

Sai dai kuma ya ce za a yi hawan Sallah da aka saba yi kowacce shekara a masarautu na jahar, yana mai cewa gwamnan jihar zai yi hawan Sallah a Kafanchan.

Wakilin BBC ya ce bisa al’ada wuraren shakatawar sukan cika makil da matasa, yara maza da mata da iyalai a lokacin bukukuwan Sallah da na Kirsimeti.

Wasu dai mutanen jihar sun yaba da matakin wanda suka ce zai hana kashe-kashen da ake samu tsakanin matasa a wajen shakatawar a lokacin bukukuwan Sallah yayin da kuma wasu ke cewa matakin takura ce ga jin dadi da kuma walwalarsu.

BBChausa.Source link

Musulman duniya na bikin babbar Sallah


Al’ummar Musulmi a fadin duniya na gudanar da bukukuwan sallar layya.

Bikin da ake kira na babbar Sallah na zuwa ne kwana guda bayan miliyoyin Musulmin da suka je aikin Hajji sun yi hawan Arafa a jiya litinin.

Wani muhimmin abu yayin wadannan bukukuwa na yau shi ne yin layya.

Bayan kammala sallar idi musulmai masu hali za su yanka dabbobin layya.

Sheikh Hussaini Zakariyya wani malamin addinin Musulunci a Najeria ya ce babban amfanin layya shi ne koyi da Annabi SAW.

Malamin ya ce ana son wadanda suka samu halin yin layyar, su taimaka wa wadanda ba su samu ikon yi ba da naman da suka yanka na layya.

Babbar sallah ko sallar layya, rana ce ta biki da murna da shagali, don kuwa ko ba komai, an shekara da rai.

Kuma a ranar Sallah akan yi ziyara ga `yan uwa da abokan arziki, tare da rarraba abinci don kara dankon zumunci.

BBChausa.Source link

Sheikh Dahiru Bauchi, Dr. Isah Aliyu Pantami da gwamnonin Yobe da na Bauchi a kasa me tsarki
Source link

Buhari ya ce hakura da yaki da rashawa cin amanar ‘yan Najeriya ne


Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba zai hakura da yaki da cin hanci da rashawa ba duk da ya janyo ma sa kiyayya da bakin jini ga wasu.

A cikin sakonsa na sallah ga al’ummar Najeriya mai dauke da sa hannun mai taimaka wa shugaban na musamman kan yada labarai Malam Garba Shehu, shugaban na Najeriya ya bukaci dukkanin musulmi su yi amfani da wannan damar domin yi nazari da yin karatun ta-natsu tare da kasancewa jekadu nagari ga addininsu ta hanyar yin aiki da koyarwarsa.

Buhari ya kuma bayyana cewa adddini wani abu muhimmi ne da ke tasiri ga halayen mutum da kuma ayyukansa.

A cikin sakon na Sallah, shugaban ya kuma bayyana damuwa da nadama kan yadda ya ce, son kai da hadama da cin hanci da rashawa ya sa wasu sun yi watsi da imaninsu domin cimma burinsu na rayuwa.

“Mika wuya ga yaki da rashawa ba zabi ba ne domin yana lalata al’umma da ci gaban kasa.”

A cewar shugaban, ” ko da kuwa yaki da rashawa ya janyo maka bakin jinni ga wasu, ba zai sa ka kariya ba a matsayinka na shugaba domin yin hakan tamkar cin amana ne ga jama’a.”

Shugaban ya bukaci ‘yan Najeriya su rungumi hanyoyi na tabbatar da zaman lafiya da hakuri da juna a kowane lokaci ta hanyar kawar da son zuciya da duk wasu bukatu na akidu ko kuma kungiyoyi.

A sakonsa na sallah ga Al’ummar musulmi, kakakin majalisar wakilai Hon Yakubu Dogara ya yi kira ga shugabannin addinai da su yi amfani da wannan lokaci domin fadakarwa kan zaman lafiya da hadin kai tsakanin ‘yan Najeriya musamman yanzu da aka shiga lokaci na siyasa yayin da zaben 2019 ke karatowa.

BBChausa.Source link

Barkanku da Sallah mabiya shafin hutudole


Assalamualaikum mabiya shafin hutudole.com gaisuwar Sallah ta musamman gareku da fatan za’a yi bukukuwan Sallah lafiya, Allah ya maimaitamana ya sa Alhazanmu suyi karbabbiyar Ibada ya kuma dawo mana dasu gida lafiya.

Ga wadanda sukayi Ibadu cikin ranaku goman nan da wanda suka yi azumi jiya da wanda zasu yi kamun baki yau, Allah yasa a dace da Ladan, ya baiwa shuwagabanninmu ikon yi mana adalci ya zaunar da kasarmu lafiya ya sadamu da dukkan alkhairai na Duniya da Lahira.

Shafin hutudole na alfahari daku.

Allah ya bar zumunci.

Barkanmu da Sallah.Source link

Tinubu Ya Taba Gulmata Mani Bai Son Salon Mulkin Buhari>>Bukola Saraki


Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya yi raddi ga Tsohon Gwamnan Legas, Bola Tinubu inda ya nuna cewa rashin tuntubarsa kan muhimman batutuwan da suka shafi kasa da gwamnatin Buhari ke yi, ya tilasta shi komawa PDP.

Ya ce, duk wadanda suka taka rawa wajen kafa gwamnatin APC wanda ya hada da mutanen jiharsa ta Kwara duk an yi watsi da su yana mai cewa, Buhari ya kan rubutowa majalisar ce kan wata bukatarsa wanda ya kamata ya fara tuntubar majalisar kafin ya rubuto.

Ya kara da cewa, ya kai wannan korafin ga shugabannin APC wanda ya hada har da Bola Tinubu wanda shi kansa ya taba nuna masa cewa ba ya son salon mulkin Buhari amma daga baya ya fahinci cewa tsohon Gwamnan Legas din na son cimma burinsa ne na zama Shugaban kasa idan wa’adin Buhari na biyu ya cika a shekarar 2023.

Rariya.Source link

Modric, Ronaldo, Salah na takarar gwarzon Uefa


An bayyana sunayen Luka Modric, Cristiano Ronaldo da Mohamed Salah cikin jerin farko na ‘yan wasan da ke takarar gwarzon dan wasan zakarun Turai, Uefa, na bana.

Kwamitin da ya kunshi alkalan wasa 80 da ‘yan jarida 55 ne ya zabi dan wasan tsakiya na Real Madrid Modric, dan wasan gaba na Juventus Ronaldo da kuma dan wasan gaba na Liverpool Salah domin yin takarar.

Za a ba da kyautar gwarzon dan kwallon kafar ne lokacin da za a yi wasannin rukuni na gasar cin kofin zakarun Turai a Monaco ranar 30 ga watan Agusta.

An bayyana sunayen Pernille Harder, Ada Hegerberg da kuma Amandine Henry domin fafatawa don zama gwarzuwar ‘yan kwallon kafar Uefa ta mata a bana.

‘Yar wasan gaba ta Denmark Harder tana buga wa Wolfsburg wasa, yayin da ‘yar wasan gaba ta Norway Hegerberg da ‘yar wasan baya ta Faransa Henry ke buga wasa a Lyon.

Ronaldo, wanda ya koma Juventus daga Real Madrid a watan Yuli a kan £99.2m, ya taba lashe gasar a 2017, yayin da Lieke Martens ta lashe gasar jim kadan bayan ta koma Barcelona daga Rosengard.

BBChausa.Source link

Akshay Kumar shi ya fi mabiya Instagram a Bollywood
Source link

Hutudole: labarai da hausa : Hafsat Idris a Muzdalifa
Source link

Wasu daga cikin jaruman fina-finan da aka yi hawan Arfa dasu a yau


A yaune akayi hawan Arfa a kasa me tsarki inda kimanin mahajjata miliyan biyu da suka fito daga kasashen Duniya daban-daban suka halarci gurin wannan babbar Ibada, daga cikin jaruman fim din Hausa da suka samu zuwa aikin Hajjin bana suma anyi wannan Ibada tare dasu.

Daga cikin taurarin akwai mawaka irinsu, Ali Jita, Nazir Ahmad Sarkin waka sai kuma me bayar da umarni, Aminu Saira, Sai jarumai, Hafsat Idris da Rahama Sadau da tsaffin jarumai irinsu, Mansurah Isah da Samira Ahmad da Saratu Gidado, Daso dadai sauransu.

Muna fatan Allah ya amsa Ibada.Source link