Taliban ta kai hari da ya nufi fadar shugaban kasa | Labarai | DW


Babu dai wasu bayanai da ke nuna cewa hare-haren sun ritsa da wani ko wani ya samu rauni kamar yadda shedu da jami’an tsaro suka fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Wani jami’in tsaro ya ce fashe-fashen sun biyo bayan wasu makaman roka da aka harbo daga wajen birnin na Kabul. Wasu rahotannin na cewa mayakan Taliban ne suka harba makaman da suka nufi fadar shugaban kasa. Harin da ke zuwa a lokacin da Shugaba Ashraf Ghani ke jawabin barka da sallah ga al’ummar Afganistan.

Mayakan Taliban sun yi watsi da bukatar da gwamnatin kasar ta Afganistan ta gabatar masu ta neman tsagaita wuta tun daga ranar Litinin wato ranar Arafat har zuwa lokacin watan Mauludi inda kungiyar ta sha alwashin ci gaba da kai hare-hare kan jami’an gwamnati da kawayensu na kasashen ketare.

 

 Source link

Al′ummar Musulmi na bikin Sallar Layya | Labarai | DW


A wannan rana ce dai ta Talata mahajjatan ke tafiya zuwa Minna don jifan shedan abin da ke tuni da sa’ilin da Annabi Ibrahim A.S shedan ya so yi masa rada lokacin da Allah SWT ya nemi ya yanka dansa Annabi Isma’il kafin daga bisani Allah Ya fanshe shi da ragon layya.

A wannan rana ta karshe a aikin Hajjin dai har ila yau al’ummar Musulmi a fadin duniya na yin sallar idi ko Eid al-Adha inda Musulmai ke yanka abin da Allah Ya huwace masu na daga dabbobi kama daga raguna zuwa shanu ko rakuma kana naman a raba shi ga al’umma marasa karfi.Source link

′Yan sandan Yuganda sun afka wa masu bore | Labarai | DW


Jami’an tsaro a Yuganda sun rufe wani bangare na Kampala babban birnin kasar tare da ‘yan harbe-harbe gami da watsa hayaki mai sa hawaye, a kokarin tarwatse wani ayarin masu zanga-zanga a wannan Litinin, tare da kama akalla mutum 70.

Masu zanga-zangar na bore ne kan tsare wani dan majalisar dokoki kuma fitaccen mawakin nan wato Bobi Wine, wanda hukumomin ke ci gaba da yi tun ranar 13 ga wannan wata na Agusta.

An dai zargi dan siyasar ne tare da wasu mutum hudu da jifan ayarin motocin Shugaba Yoweri Museveni a yankin arewa maso yammacin kasar, lokacin wani gangamin yakin neman zabe.

Tsare Bobi Wine din wanda babban mai adawa ne da Shugaba Museveni, na ci gaba da tunzura jama’a da dama a Yugandar, inda ake ta kone-kone a wasu manyan titunin birnin na Kampala.Source link

Saudiyya:Miliyoyin mahajjata sun hau Arafat | Labarai | DW


Tsayuwa a kai ko gefen dutsen Arafat a ranar tara ga watan Zul-Hijja na zama kololuwa da kuma ya wajaba a kan dukkan Mahajjata.

A rana mai kamar ta yau kimanin shekaru 1,400 da suka gabata, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, ya gabatar da hudubarsa ta karshe a dutsen na Arafat.

Ana dai son dukkannin Mahajjata su gabatar da addu’o’i na musamman a wannan rana.

Kwana guda gabannin ranar hawa Arafat, an yi ruwan sama da guguwa mai karfi da ta lalata tantunan Mahajjata amma hukumomi sun ce ba wanda ya ji rauni.Source link

Najeriya ta amince da hukuncin FIFA | Labarai | DW


Najeriya ta amince da shugabancin hukumar kwallon kafa na kasar da hukumar kwallo ta duniya FIFA ta yarda da shi, ‘yan mintuna gabanin cikar wa’adin haramta mata shiga manyan gasannin duniya nan gaba.

Dama dai da misalin karfe 12 agogon Najeriyar na wanna Litinin ne wa’adin na FIFA zai cika, kan daukar matakin saboda sa baki da hukumomi suka yi kan zaben jagororin hukumar wasannin kasar da aka yi a baya.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na twitter, mai magana da yawun mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce Najeriyar ta aike wa FIFA cewar ta amince da jagorancin hukumar ta NFF karkashin Amaju Pinnick.

Da fari dai FIFA ta shirya hana Najeriyar shiga wasannin neman shiga gasar cin kofin kasashen Afirka ne da za a yi cikin watan gobe.Source link

An kai hari a ofishin jakadancin Amirka da ke Turkiyya | Labarai | DW


Rahotanni daga kasar Turkiyya na cewa wasu dauke da bindigogi sun buda wuta kan ofishin jakadancin Amirka da ke a kasar, sai dai babu labarin wani da halaka a lamarin.

A cewar jami’an jakadancin Amirka a Turkiyyar da ma wasu na gwamnatin kasar, da jijjifin safiyar wannan Litinin ‘yan bindigar suka harba harsasai sau shida daga cikin wata motar da ke wucewa ta ofishin wanda ke Ankara babban birnin kasar.

Kakakin gwamnatin Shugaba Racep Tayyip Erdogan, Ibrahim Kalin, ya bayyana hakan da cewa wani yunkuri ne na ta’azzara lamura tsakanin Turkiyya da Amirka, da a yanzu ke takaddamar cinikayya da ta diflomasiyya.

Ofishin jakandancin na Amirka wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce babu wani da ya mutu ko ya ji rauni, tare kuma da yaba wa jami’an ‘yan sandan Turkiyyar da irin binciken da suke gudanarwa a kan harin.Source link

An kai hari a ofishin jakadancin Amirka | Labarai | DW


Rahotanni daga kasar Turkiyya, na cewa wasu dauke da bindigogi sun buda wuta kan ofishin jakadancin Amirka da ke a kasar, sai dai babu labarin wani da halaka a lamarin.

A cewar jami’an jakadancin Amirka a Turkiyyar da ma wasu na gwamnatin kasar, da jijjifin safiyar yau ne ‘yan bindigar suka harba harsasai sau shida daga cikin wata motar da ke wucewa ta ofishin wanda ke Ankara babban birnin kasar.

Kakakin gwamnatin Shugaba Racep Tayyip Erdogan, Ibrahim Kalin, ya bayyana hakan da cewa wani yunkuri ne na ta’azzara lamura tsakanin Turkiyya da Amirka, da a yanzu ke takaddamar cinikayya da ta diflomasiyya.

Ofishin jakandancin na Amirka wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce babu wani da ya mutu ko ya ji rauni, tare kuma da yaba wa jami’an ‘yan sandan Turkiyyar da irin binciken da suke gudanarwa a hkan harin.Source link

Saudiyya:Miliyoyin mahajjata su hau Arafat | Labarai | DW


Tsayuwa a kai ko gefen dutsen Arafat a ranar tara ga watan Zul-Hijja na zama kololuwa da kuma ya wajaba a kan dukkan Mahajjata.

A rana mai kamar ta yau kimanin shekaru 1,400 da suka gabata, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, ya gabatar da hudubarsa ta karshe a dutsen na Arafat.

Ana dai son dukkannin Mahajjata su gabatar da addu’o’i na musamman a wannan rana.

Kwana guda gabannin ranar hawa Arafat, an yi ruwan sama da guguwa mai karfi da ta lalata tantunan Mahajjata amma hukumomi sun ce ba wanda ya ji rauni.Source link

Saudiyya: Mahajjata na hawan Arafat | Labarai | DW


Tsayuwa a kai ko gefen dutsen Arafat a ranar 9 ga watan Zul-Hijja na zama kololuwa da kuma ya wajaba a kan dukkan Mahajjata.

A rana mai kamar ta yau kimanin shekaru 1,400 da suka gabata, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, ya gabatar da hudubarsa ta karshe a dutsen na Arafat.

Ana dai son dukkannin Mahajjata su gabatar da addu’o’i na musamman a wannan rana.

Kwana guda gabannin ranar hawa Arafat, an yi ruwan sama da guguwa mai karfi da ya lalata tantunan Mahajjata amma hukumomi sun ce ba wanda ya ji rauni.Source link

Tsagaita wuta a rikicin Afghanistan | Labarai | DW


Shugaban ya ambata hakan ne a wani jawabi da ya yi wanda aka yada shi ta gidan talabijin din kasar inda ya ke cewar shirin tsagaita wutar zai fara ne daga Litinin 20 ga wannan watan na Agusta da muke ciki zuwa ranar Talata 20 ga watan Nuwamban da ke tafe.

Baya ga batun tsagaita wutar, Shugaba Ghani ya bukaci ‘yan kungiyar ta Taliban da su yi amfani da wannan lokaci wajen hawa kan teburin sulhu da hukumomin kasar don kawo karshen rikicin da suke yi. Ya zuwa yanzu dai Taliban din ba su kai ga cewa komai ba kan hakan. Wannan dai shi ne karo na biyu da gwamnatin ta Afghanistan ke shiga irin wannan yarjejeniya da kungiyar gabannin bukukuwan babbar sallah.

 Source link