Bukatar Dakile Yawaitar Kananan Makamai A NijeriyaYawan amfani da muggan makamai a yayin rikice-rikice a kasar alami ne na yawann kananan makaman dake jibge a hannun mutane a lungunan kasar nan. Mutane da kungiyoyi da dama da basu da alaka da hukuma na rike da makamai ba tare da cikkaken izini ba wannan kuma na jawo asarar rayuka da dukiyoyin jama’a a kullu wani rikici ya tashi.

A shekara 2016 rahoton majalisar dinkin duniya ya nuna cewa, kashi 70 na kiyasin da aka yi na makamai Miliayan 500 dake yawo a yankin Afika ta yamma suna jibge ne a kasar mu Nijeriya, shekara biyu da suka gabata a jihar Ribas  kadai an karbi makamai fiye da 22,430 daga hannun ‘yan taratsin Neja Delta da ‘yan ta’adda da ‘yan kungiyoyin asiri lokacin da suka rungumi ahuwar da gwamnati ta yi musu, sun mika bindigogi 1,000 da albarushai 7,661 da bamabamai 147.

A shekarar da ta gabata majalisar dattijai ta nuna damuwar ta a kan karuwar yawaitar kananan makamai a tsakanin ‘yan Nijeriya.

A na danganta yawan shigowar makamai kasar nan saboda rikice- rikicen da ke faruwa a kasashe makwabta musamman irinsu kasashen Libya da Chadi da rikicin Boko Haram da kuma ‘yan taraytsin  Neje Delta, dole a dora wanna sakacin a kan jami’an tsaro tun da su ne ke da alhakin kare iyakokin kasar da kuma cikin kasar baki daya. Mutane kadan ne suka san da zaman hukumar nan ta musamman da aka kafa domin sa ido a kan yaduwar kananan makamai a kasar nana mai suna “National Commission on Small Arms and Light Weapons, NATCOM” wanna kwananar ta yi korafin cewa, duk da yarjejeniyoyin da ake dasu da kasashen yankin  Afrika ta yamma na ECOWAS babu abin daya canza na sanya ido a kan iyakar kasashen domin dakile safarar kananan makamai tsakanin ksashen. Hukumar NATCOM ta tabbatar da cewa, saboda rikice-rikicen daya ki ci ya cinye wa a yankin Afrika da kuma rikicin Boko Haram na Arewacin Nijeriya an gano sakacin jami’an tsaronmu na gazawar da suka yi na sanya ido da dakile zirga zirgan kananan makamai a cikin Nijeriya. Rashin kyakyawan sanya ido a iyakokin kasaar nan da iyakokin jihohi ya sanya al’amarin ya zama mai sauki ga masu fataucinn muggan makamai, amfani da ake a kai tsaye da makamai a rikicin daya ke aukuwa tsakain makiyaya da manoma a ‘yan kwanakin nan alami ne na yadda makamai ke dankare a hannun jama’a.

Wadannna yana sanya harkar tsaron kasa cikin garari da kuma rayuwar ‘yan kasa cikin hatsari, domin kuwa da zaran an dan samu hatsaniya zaka ga makamai na yawo kamar an buga gangar yaki abin dake sanya raywar wadanda basu jiba basu gani ba cikin hatsarin rasa rayuwar su da kuma dukiyoyinsu. Masana na da ra’ayin cewa, a kwai bukatar gwamnati ta kara karfin jami’an tsaron dake lura da tsaron iyakokin mu da kuma na cikin kasa a kuma yi amfani da jami’an tsaro na farin kaya wajen sunsuno masu safarar makamai da inda suke boye su, gwamnati na kuma iya amfani da tsarin na marigayi shugaba Umaru Musa Ya’adua inda ya sanya lada na musamman ga duk wanda ya mika makaminsa.

Dole dukkan hukumomin gwamnati su kara kaimi wajen ba mara da kunya a yaki da kuma kawar da kanannan makamai a tsakanin al’umma domin tsaron kasa aiki ne daya rataya a kan kowa da kowa.

Sashi na 146 na dokan hurda da makamai na gwamnatin tarayya Nijeriya ta shekarar 1990 ta bayar da amincewar tag a dan kasa ya mallaki makami domin kare kansa daga kowanne nau’in barazana ko harin da aka iya kawo masa, dokan ta ci gaba da yin karin bayani a kananan sashi na

31 da 32 da kuma na 33.

A lokuttan baya gwamnati ta yi yekuwa ga ‘yan kasa dasu mika makaman dake hannuna bisa radin kansu ga hukumomi, an yi irn wanna shirin a shekarun 2002 da 2003 da kuma 2004 in da aka karbi makamai da suka kai sama da 1,90260 a shekarar 2003 da sama da 1,46661 a shekarar 2004, hukumomi sun lallata makaman, wannan mataki ne mai mahimmanci a hankoron da ake yin a rage bazuwa da yaduwar makamai a Nijeriya.

Dokar ta yi bayani dalla-dalla a kan cewa duk wani makami da aka kama dole a lallata su ba wai a sake mayar dasu ga jama’a ba, a kwai horon zama gidan yari na shekara 5 ga wanda aka kama yana dauke da makami ba tare da izini ba.

Dokar ta kuma bayar da izinin rike makami a fili matukar mutum na da lasisin yin haka, dokar ta kuma haramta tafiya da makami a boye koda kuwa a kwai izinin rike makamin.

Ya kamata kwamitin shugaban kasa a kan kananan makamai “The Presidential Committee on Small Arms and Light Weapons, PRESCOM” ta kara kaimi wajen yin aikin da dokar da ta kafa ta aiyana na fuskantar dakile yawaitar kananann makamai a cikin kasa, a kwai bukatar kwamitin ta yi aiki tare da hada hunnu da majalisar dokoki na tarayya domin kawo gyare-gyare a dokokin dake lura da hurda da makamai wannada a ka kirkiro tun a skekara 1959 wannda aka kuma yi wa gyara a shekarar 2014 tabbas lokaci ya yi da za a sake nazarin dokar domin samar da hukunce -hukuncen da zasu yi dai da matsalolin da ake fuskanta na yawan makamai a tsakain alumma. Sakamakon taron kasar da hukumar PRESCOM ta gudanar a shekarar 2014 yana da mahimmanci, ya kamata a dauko shi domin aiwatar da shi hakan zai karfafa zuciyar jama’a domin idan ba a yi hankali ba mutane zasu kara zafafaf kokarin malakar makamai domin kare kansu daga hareharen da ke yawan faruwa da kuma kare kai daga harin yan fashi da makamai da masu garkuwa da mutane. Idan abin ya tafi a haka za a kai ga yanayin da iyalai da alummun da garuruwa zasu ringa hada kai domin sayan makaman da zasu kare kansu daga yiwuwar kawo musu hari domin kare rayuwarsu da tana iyalansu.

 

What's Your Reaction?

Angry Angry
0
Angry
Cute Cute
0
Cute
Fail Fail
0
Fail
Geeky Geeky
0
Geeky
Lol Lol
0
Lol
Love Love
0
Love
OMG OMG
0
OMG
Win Win
0
Win
WTF WTF
0
WTF

Comments 0

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Bukatar Dakile Yawaitar Kananan Makamai A Nijeriya

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format