Boko Haram ta kai hari kusa da Maiduguri


Harin Boko Haram a DaloriHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Akalla mutum 12 Boko Haram ta kashe a harin da ta kai Dalori a karshen Oktoba

Wasu mahara da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun kai hari a wasu kauyuka biyu da ke kusa da garin Maiduguri.

Harin wanda ake ganin wani yunkuri ne na kokarin shiga Maiduyguri ya tilastawa mazauna kauyukan tserewa daga gidajensu.

Rahotanni sun ce an kai harin ne da yammacin jiya Asabar a unguwar Polo da ke wajen Maiduguri da kuma wasu kauyuka biyu Bale Shuwari da Jimine da ke bayan Giwa Barracks da Boko Haram ta sha kai hare hare.

Mazauna yankin sun ce an shafe lokaci suna jin karar harbe harbe da tashin bama-bamai, lamarin da ya firgita su suka tsere daga gidajensu, kamar yadda wani mazauni yankin ya shaidawa BBC.

Ya ce kura ta lafa a Polo bayan da ya dawo gidansu a cikin dare kuma ya ga jami’an tsaro a unguwar bayan kai harin.

Rahotanni sun ce sojoji ne suka kori maharan bayan sun yi musayar wuta da su. Sai dai babu wata sanarwa da ta fito daga rundunar sojin kasar game da harin.Source link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *