Bishop 39 na son ajiye aiki a Chile | Labarai | DW


Dukkannin manyan limaman cocin kasar Chile 34, sun mika takardaun ajiye aiki ga shugaban darikar katolika na duniya Paparoma Francis, bisa zargin lalata da cin zarfi a fadin kasar.

Ganawar paparoman da limaman Cocin ya biyo bayan binciken fadar Vatican ta yi kan rufa-rufa a kan aikata lalata da cin zarafi a kasar, ciki har da nadin da Paparoman ya yi wa Boshop Juang Barros a 2015 duk da zargin lalata da ake a kanshi.

A wata sanarwa da limaman Cocin suka fitar, sun nemi afuwar ‘yan kasar da kuma iyalan wadanda abin ya shafa tare da cewa suna jiran matakin da Paparoman zai yanke kan bukatun ajiyae aikin.Source link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *