Ba Maganar Janye Yajin Aiki A Jami’ar ABU Zariya, Inji kwamared Sha’aibu KhalilDa sanyi safiyar Litinin nan ne shugaban riko na kungiyar ma’aikatan jami’o’i na kasa reshen jami’ar Ahmad Bello Zariya Kwamred Sha’aibu Kalil ya shelanta ci gaba da yajin aikin da kungiyar take ciki a hanlin yanzu a fadin kasa baki daya.

Kwamred Sha’ibu ya jaddada hakanne a gaban dimbin ‘yan kungiyar da suka halacci taron a harabar jami’ar dake samarun Zariya, ya kuma yi dogon bayani a kan fafutukar da suke gudanarwa tare da shugabanin kungiyar ta kasa don samun nasarar a kan gwamnati.

Daga cikin albishir din da shugabannin gamaiyar kungiyoyin suka gabatarwa ga ‘yan kungiyar shi ne suyi hakuri hakar su ta kusan cimma ruwa domin gwamnati ta yi motsi amma motsin bai gamsar da wakilan su ta kasa ba duk da cewa sun nemi ta kara motsawa, ya ce suna sa ran za su sami nasara bisa ga yadda lamarin fafutukar ke gudana a halin yanzu tun daga kasa har zuwa sama.

Daga Karshe ne shugaban mata ta kungiyar ta SANNU ta kasa Barista Hadiza Kabiru, ta jadda ciga ba da yajin aikin har sai wakilansu na kasa sun basu umurnin janyewa  kuma ta yi jinjina ga wakilai na shiyyoyi bisa jajircewarsu a kan ganin gwamnati ta biya musu bukatunsu ta ce, bada jimawa ba kowa zai ji alat daga abin da aka farauto, ta ce asa a baka yafi a rataya.

Barista Hadiza ta ja hankalin ‘yan kungiyar da su guji amfani da surutan baragurbin da suke kawo wa kungiyar matsaloli duk abin da suka ji to suyi bincike in har ba daga shugabanin su na kasa bane to suyi watsi da shi .

Kuma ‘yan kungiyar sun koka matuka a kan yadda hukumar tsaron jami’ar suke takura musu a wajen da suke gudanar da harkokin kungiyoyin su.

Kanar Tukur shi ne shugaban sashin tsaro na jami’ar ta ABU ya yi bayani a kan wannan zargin da ake musu, ya ce, “A gaskiya bamu takura wa kowa mu aikinmu mu ke yi”

Ya zuwa hada wannan labarin bincike ya nuna cewa da yawa daga cikin ma’aikatan jami’ar sun marawa ci gaba da yajin aikin baya

What's Your Reaction?

Angry Angry
0
Angry
Cute Cute
0
Cute
Fail Fail
0
Fail
Geeky Geeky
0
Geeky
Lol Lol
0
Lol
Love Love
0
Love
OMG OMG
0
OMG
Win Win
0
Win
WTF WTF
0
WTF

Comments 0

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ba Maganar Janye Yajin Aiki A Jami’ar ABU Zariya, Inji kwamared Sha’aibu Khalil

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format