Auren ‘Yar Gwamnan Kano Da Na Oyo Zai Karawa Hausawan Kurmi Tagomashi- Sarkin Samarin Hausawa Na OyoDaga, Na’ima Abubakar  Kano.

Mai martaba Sarkin Samarin Hausawan Jihar Oyo Alhaji Muhammadu Nasiru Yaro, ya bayyana auren diyar gwamnan Kano da na gwamnan jihar Oyo wanda ya gudana a makon jiya abin farin ciki ne wanda zai karawa ‘yan Arewa mazauna jihohin yamma “kurmi” tagomashi mussamman ma hausawa mazauna jihar ta Oyo.

Sarkin samarin yace auratayya a tsakanin kabilu mabanbanta ba bakon abu bane a tsakanin Hausawan jihar Oyo, Yarbawa ko sauran kabilun yankin ba, domin  tun a zamanin kakkanin mu akwai auratanya a tsakanin hausawa da yarbawa wannan kyakyawar alaka ta taka muhinmmin rawar gani wajen kulla kyakayawar alakar kasuwanci da zamantakewa a tsakanin kabilun biyu, wannan ya taimaka mana kwarai wajan ƙara samun fahimtar juna da zaman lafiya tare da sanin al’adun juna

Sarkin samarin hausawan na jihar Oyo yayi kuma Kira ga al’umma su mayar da hankulan su akan alfanun da zai biyo bayan auren ba wasu kura-kuren da aka yi ba, wannan abu ne da zai kara kyakyawar alaka a tsakanin Hausawa da Yarbawa  da kuma hadin kai da za’a samu a siyasance gabanin zaben 2019. Wannan auren Na yayan manyan ‘yan siyasa na Kudu da Arewa  wannan abin alfahari ne, kuma wannan shine koyarwar addinin mu na musulumci wanda a ko wane lokaci yake yaki da kabilanci, domin musulmi ‘yan uwan juna ne ba tare da la’akari da bambamce-bambamce kabila ba, irin wannan mu’ammala zata kara mana fahimtar juna tare da sanin al’adun mu yadda ko wane zai girmama ɗan uwansa tare sanin alfanin zama daya al’umma daya.

Sarkin samari Alhaji Muhammadu Nasiru Yaro yayi fatan samun kwanciyar hankali da zaman lafiya ga ma’auratan tare da fatan alakar ta zamo alkhairi ga al’umomin jihar Kano da na Oyo dama kasa baki daya, yanzu gwamnonin Kano dana Oyo sun bude kofar cigaba da samun irin wannan auratayya a tsakanin kabilun kasar nan kuma abu ne da zai bada  gagarumar gudun mawa wajen dunkulewar kasar nan  a matsayinta na kasa daya al’umma daya.

What's Your Reaction?

Angry Angry
0
Angry
Cute Cute
0
Cute
Fail Fail
0
Fail
Geeky Geeky
0
Geeky
Lol Lol
0
Lol
Love Love
0
Love
OMG OMG
0
OMG
Win Win
0
Win
WTF WTF
0
WTF

Comments 0

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Auren ‘Yar Gwamnan Kano Da Na Oyo Zai Karawa Hausawan Kurmi Tagomashi- Sarkin Samarin Hausawa Na Oyo

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format