Amirka: Mace ta zama shugabar hukumar CIA | Labarai | DW


 

An sami sabanin ra’ayi bisa nadin matar mai shekaru sittin da daya a sanadiyar zarge-zarge da ake ma ta na gallazawa wasu mutane da aka tsare bayan munmunar harin da aka kai wa Amirka na 9/11 a shekarar 2001.

Shekaru akalla talatin da uku ta kwashe tana aiki a karkashin hukumar kafin wannan mukami, ta kuma maye gurbin Mike Pompeo wanda shi ne sakataren harkokin wajen Amirka a yanzu. Bayan da aka amince da nadin Haspel, kungiyar kare hakkin bil adama ta Human rights ta fidda sanarwa inda ta soki matakin bai wa matar da ta ce ta aikata laifi da keta haddin bil’adama.

 Source link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *