Allah Ya Yiwa Shahararren Masanin Kimiyya Stephen Hawkins Rasuwa (Hotuna)Allah ya yiwa shahararren masani a harkan kimiyya, Stephen Hawkins, rasuwa.

 

Stephen Hawkins ya rasu ne a 14 ga watan Maris 2018 da shekaru 76.

 

An samu labarin ne a wani sanarwa da ‘ya’yansa Lucy, da Robert, da kuma Timothy, suka fitar a safiyar yau mai cewa, “Muna bakin cikin sanar da rasuwan mahaifin mu a yau. Ya kasance babban masani a harkar kimiyya wanda za a ci gaba da nazari a kan ayyukansa. Karfin hali da juriyansa tare da iliminsa da mutuncinsa ya kasance wahayi ga mutane da dama a fadin Duniya. Za mu ji kewan shi har abada”.

 

Karanta wannan: ‘Yan Bindiga Sun Sace Uwargidan Wani Dan Majalisa

 

Hawkins kafin rasuwansa ya kasance nakasasshe ne bayan ya kamu da cutar da masani ke kira da suna ALS a lokacin da ya ke shekara 21 a Duniya dan watanni kadan da shiga jami’a . ALS wani irin cuta ne mai kashe jijiyoyin da ke sanya mutum yayi motsi.

 

Bayan cutar ta nakasa shi, Hawkins ya zo bai iya cin abinci, balantana ma ya iya komai da kansa, ya kuma ana yi masa komai ne kamar yadda ake wa jariri.

 

Karanta wannan: Shugaba Buhari Ya Yabawa Manoma (Hotuna)

 

Amma duk da hakan, cutan bai hana Hawkin yin aure da haihuwa ba. A nan ne ya aure matarsa ta farko Jane Wilde a shekarar 1965 wadda ta haifar masa ‘ya’ya 3 – Robert, da Lucy da kuma Timothy, kafin su rabu a shekarar 1995. Hawkins da matarsa ta farko, Jane.

 

Bayan ya rabu da matarsa ta farko, Hawkins a shekarar 1995 ya sake yin wani aure inda ya aure mai jinyarsa Elaine Mason. Auren wanda ya dauke tsawon shekaru 11 kafin su rabu da juna.

Hawkins da Elaine

A shekarar 2009, Hawkins yayi ritaya daga koyarwa a matsayin Farfesa na ilimin lissafi. A lokacin ma bai ko iya motsi da kujerar nakasassun da aka masa.

 

Karanta wannan: Ministan Albarkatun Ruwa Ya kaddamar Da Aikin Samarda Tsabtataccen Ruwansha

 

Hawkins ya samu lambar yabo da dama a fadin Duniya. Kafin rasuwanta, Hawkins ya rubuta litattafai da dama tare da samar da wasu sabin karin haske a bangaren kimiyya da a Duniya.

 

 

Post Views: 35

What's Your Reaction?

Angry Angry
0
Angry
Cute Cute
0
Cute
Fail Fail
0
Fail
Geeky Geeky
0
Geeky
Lol Lol
0
Lol
Love Love
0
Love
OMG OMG
0
OMG
Win Win
0
Win
WTF WTF
0
WTF

Comments 0

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Allah Ya Yiwa Shahararren Masanin Kimiyya Stephen Hawkins Rasuwa (Hotuna)

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format