Abinda ya kaini ofishin DSS>>Oshiomhole


Bayan dawowarshi Najeriya daga kasar waje, shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole ya bayyana gaskiyar lamari akan kamun da hukumar ‘yansandan farin kaya ta DSS tamai.

Oshiomhole ya bayyana cewa, da kanshi ya amsa gayyatar ta DSS yakai kanshi ofishinsu kuma abinda suka tattauna shine maganar zaben fidda gwanin ‘yan takarkarun APC ne da akayi a fadin kasarnan.

Saidai Oshiomhole yace, ba hurumin DSS bane shiga maganar zaben fidda gwani na jam’iyya ba ko kuma maganar rashawa da cin hanci ba, idan ana maganar cin hanci, EFCC ko ICPC ne ya kamata su shigo ciko.

Ya kuma karyata rade-radin da akaita yaya tawa cewa wai wuta yaji daga hannun gwamnoni da DSS shiyasa ya arce daga kasar da kuma wai DSS din sun ce ya dawo washe gari amma yaki ya tafi kasar waje.

Yace yaje kasar Amurka ganin matarshi ne daga nan kuma ya wuce Ingila inda suka gana da Bola Tinubu.Source link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *