1509476657_2017-10-31-17_25_17.jpg

Ali Nuhu da Hadiza Gabon

Taurarin fina-finan Hausa Ali Nuhu(Sarki) da Hadiza Gabon kenan a wannan hoton nasu daya kayatar, muna musu fatan Alheri.

PHOTO-FOR-INSIDE-BIZ.jpg

USAID Da NESTLE Sun Horar Da Manoma Da Malaman Gona Daga Abubakar Abba, Kaduna Fannin ci gaban ƙasa da ƙasa na ƙasar amurka USAID da wasu ƙungiyoyi guda uku daga yanzu zasu dinga horar da manoma da malaman gona akanmatsakaitun aikin noma da harkar kasuwanci a jihar. Hakan yana ƙunshe ne a cikin sanarwar da ƙungiyoyin suka sanyawa hannu suka kuma raba manema labarai. Sauran ƙungiyoyin uku sune, kamfanin Nestlé da ƙungiyar sa kai ta inganta tattalin arzikin ƙasa da kuma ƙungiyar ƁEGA. An ruwaito cewar, ƙungiyoyin zasu dinga gudanar da shirin ne a ƙarƙashin sabuwar haɗaka ta mai taken,” ciyar da ƙasa abinci da masarar Nestlé mai ƙarko don inganta haɗin gwaiwa.” Taron da mahimmancin gaske kasancewar yin girbi na farko, ana samun asara da kuma sauran ƙalubale da ake fuskanta na amfanin gona kamar na waken soya da masara da ke zamowa matsala ga ƙananan manoma har su kasa samun wani jarin azo a gani. Gurɓatar amfanin gona, yana shafar lafiyar alumma harda da rayukansu da kuma lafiyar dabbobi, inda hakan ke janyo ciwon cutar daji data ƙoda da liba. Sanarwar taci gaba da cewa,I hakan na kuma shafar lafiyar yara, kamar shafar girmansu da kuma sanya masu cututtuka. Sun bayyana cewar, manoman zasu koyi ilimin yadda zasu magance gurɓacewar amfanin na gona don samar da ingantacciyar masara da waken soya da zasu ƙarawa alummar ƙasar nan lafiya. Akan haɗin gwiwar kuwa, Darakta a USAID Stephen Haykin, ya sanar da cewa, haɗakar tsakanin masa’antu masu zaman kansu da ɓangaren gwamnati zai taimaka wajen ragewa manoman talauci ta hanyar koyar dasu dabarun noma na zamani da kuma samar masu da kuɗin shiga. Ya ƙara da cewa horarwar kuma za ta basu ilimi wajen inganta amfanin gonar su. Shima a nashi jawabin, Manajin darakata na kamfanin Nestlé Mista Mauricio Alarcon, ya ce, haɗakar anyita ne a bisa ƙa’idojin kamfanin musamman don inganta lafiyar ‘yan baya, inda ya yi nuni da cewa, “ ayau a cikin gida ana samar da kayayyakin sarrfawa sama da kashi 80 bisa ɗari, kuma a shirye muke da mu ƙara haɓaka hakan a ƙasar nan.” Ya ci gaba cewa“ munyi imanin cewar haɗakar da alumma da ƙungiyoyin za ta taimaka wajen inganta rayuwar alumma da suka suka shafi ayyukan mu.” Shi ma shugaban ƙungiyar CNFA kuma babban jami’i Sylɓain Roy ya bayyana cewar haɗakar za ta taimkawa ƙungiyar tasu, wajen samar da ƙwararru don taimakawa ƙananan manoman dake ɗaukacin faɗin duniya, ya ƙara da cewa, ƙungiyar tasu a shirye take wajen ganin ta samar da canji mai amfani. Haka shima shugaba kuma jami’i a ƙungiyar ƁEGA Michael Deal, ya nuna jin daɗinsa a bisa haɗakar, inda ya ce hɗakar za ta samar da mafita da ci gaba ga ƙananan manoma dake ƙasar nan da kuma iyalai. A ƙarshe ya bada tabbacicn cewar, ƙungiyar tasu za ta ci gaba da tabbatar da haɗakar musamman don a samu sakamako mai amfani. Musulunci Ya Amince Da Allurar Rigakafin Shan Inna –Sarkin Musulmi Daga Abubakar Abba, Kaduna Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ƙara tabbatarwa da alummar ƙasar nan cewar Allurar rigakafin cutar shan Inna bata da wata illa ga yara ƙanana da magance cututtuka shida masu saurin hallaka yara kuma addinin Musulunci, ya amince da yin rigakafin cutar. Abubakar ya sanar da hakan ne lokacin da yake jawabinsa a shalkwatar Ƙaramar Hukumar Wamakko dake cikin jihar Sokoto lokacin gangamin yaki da cutar na ƙasa. Ya ce,” Allurar ta shan inna da kuma sauran cututtukan dake sauran hallaka yara ƙanana kamar su ƙyanda da kwalara da tarin fuka da sauransu basu da wata illa ga yaran.’’ Sarkin Musulmi ya ci gaba da cewa,“ Likitocin duniya da kuma Malaman addinin Musulunci, sun amince da Allurar akan cewar bata da wata illa ga yara ƙanana.” A cewar shi, “mun kuma amince da abin da suka ce, domin ba zamu bari a yi wa yaranmu abinda zai cutar da lafiyarsu ba.” Alhaji Abubakar ya yi kira ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya dasu karɓi Allurar hannu bibiyu haka kuma mata masu juna biyu kada suyi sake, wajen zuwa yin awo da kuma zuwa sauran gwaje-gwaje da ake yi wa masu juna biyu. Sarkin ya kuma ƙara jadda da ci gaba da bada goyon bayan masu riƙe da muƙaman gargajiya dake Arewacin ƙasar nan, akan yaƙar cutar da kuma sauran cutttuka shida masu sauran hallaka yara a ƙasar nan. A nashi jawabin a waurin taron, Gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal, ya yabawa Gwamnatin Tarayya da Sarkin Musulmi da kuma sauran masu ruwa da tsaki, a bisa gagaruwar gudunmawar da suke badawa akan faɗakar da iyayen na su miƙa ‘yayansu don ayi masu Allurar cutar. Tambuwal ya bada tabbacin cewar, gwamantinsa, baza tayi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da bada gudunmawa da goyon baya don cakkafe cutar baki ɗaya a jihar ta Sokoto da ƙasa baki ɗaya. Gwamnan ya ci gaba da cewa, gwamnatinsa a shirye take don taga ta cika alƙawurranta na dukkan yarjejeniyar data kulla a kan ko wanne fanni, harda fannin lafiya a jihar. Ya yi nuni da cewa,“ shi yasa gwamnatin jihar, ta warewa harkar lafiya har kashi sha shida bisa ɗari a cikin kasafin kuɗinta na shekarar 2017.” Gwamnan ya kuma sha alwashin magance dukkan ƙalubalen da fannin lafiya ke fuskanta a da nufin ƙara bunƙasa fannin a jihar. Shi kuwa, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa na Matakin Lafiya ta Farko na Ƙasa da kuma sauran cututtuka da za a iya yaɗa su, Sanata Mao Ohuabunwa, ya bayyana cewar Majalisar tana san rai wajen ganin cewar ƙasar nan ta fita daga cikin sahun sauran ƙasashen dake fama da cutar. Shi ma Shugaban Kwamitin Lafiya na Majalisar Wakilai Mista Chike Okafor wanda Mataimakinsa Alhaji Mohammed Usman ya wakilta a wurin taron, ya bayyana cewar, kwamtin zaici gaba da sanya ido, don ganin ana tura kuɗi a ɓangaren harkar lafiya a ƙasar nan, musamman don inganta lafiyar ‘yan Nijeriya.

PIC.1. FARMERS WORKING ON A RICE FARM IN ZUMBA, NIGER STATE ON SUNDAY (11/9/11). USAID Da NESTLE Sun Horar Da Manoma Da Malaman Gona Daga...

170428100933-trump-white-house-0425-1024x576.jpg

Baƙuncin Amurka (II)

tare da: Ibrahim Mohammed Aboki [email protected] Tattalin Arziki An yi ittifaƙi na gama gari, wanda babu wani ɗaya tilo ko gungu na mutane da ke jayayya da...

Sen.-Ahmed-Makarfi.jpg

Ƙungiyar TNG Za Ta Yi Taro A Jos

Daga Lawal Umar Tilde, Jos ‘Ya’yan ƙungiyar, “The Transform Nigeria Group [TNG]’, ƙarƙashin jam’iyyar PDP ta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da taron shiyyar Arewa ta...

1509401956_2017-10-30-14_07_26.jpg

Ali Nuhu a Ingila

Tauraron fina-finan Hausa Ali Nuhu (Sarki) kenan a kasar Ingila inda ya kai ziyara, A jiyane dai Alin ya hadu da abokinshi kuma tauraron kwallon...

log in

Captcha!

reset password

Back to
log in
Choose A Format
Gif
GIF format