Oyetola ya lashe zaben fidda gwanin takarar gwamnan jihar Osun a karkashin jam’iyar APC

Isiaka Oyetola, shugaban ma’aikatan gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, shine mutumin da aka bayyana ya lashe zaben fidda gwanin jam’iyar APC na takarar kujarar gwamnan jihar.

Oyetola zai kasance wanda zai wa jam’iyar APC mai mulkin jihar takara a zaben gwamnan da za a gudanar ranar 22 ga watan Satumba.

Ya samu kuri’a 127,017 inda ya kayar da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Yusuf Lasun wanda ya samu kuri’a 21975 a zaben.

Najeem Salam kakakin majalisar dinkin dokokin jihar shine ya zo na uku a zaben da ƙuri’u 17958.

Zaɓen ya gudana ne karakashin jagorancin gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari.

Wasu yan takara a zaben , ciki har da sakataren gwamnatin jihar sun fice daga zaɓen bayan da suka yi zargin cewa ba za a yi musu adalci ba.
Source link

‘Dan sanda ba abokin gaba bane’


Nigeria Police on duty

Image caption

‘Yan sandan Najeriya

Sha’anin tabarbarewar tsaro ya ci gaba da sanya damuwa a Najeriya, har wasu kungiyoyin dattijai sun gudanar da taron nufin lalubo hanyoyin magance wannan al’amari.

Wasu dai na ganin matsalar ta samo asali ne sakamakon rikon sakainar kashi da aka yi wa aikin ‘yan sanda tsawon lokaci.

Rahotanni sun ce ana samun korafe-korafe na rashin biyan hakkokin aiki a kan lokaci da kuma rashin bai wa rundunar ‘yan sandan isassun kudin da za ta tunkari kalubalan tsaron da ke tasowa.

Mallam Sulaiman Abba, tsohon babban sufeton ‘yan sanda ne, kuma ya gabatar da mukala yayin taron.

Ya kuma shaidawa BBC daya daga cikin matsalolin da suke janyowa aikin dan sanda mummunanr fahimta shi ne rashin jituwa tsakanin su da al’umar da suke karewa.

”Shekaru da dama da suka gaba a matsayi na ma’aikacin ‘yan sanda da ke tasre dukiyar al’uma, ina ganin abin da ya janyo lalacewar aikin dan sanda shi ne rikon sakainar kashi da ake yi wa aikin.”

Ya kara da cewa: “Tsarin mulki ya bai wa dan sanda damar kare jama’a da dukiyarsu. Sai da aka fadi dan sanda kafin wani.

Ya kuma ce, “Dokoki sun bayyana aikin dan sanda shi ne kama masu laifi ta hanyar bincike da gurfanar da su gaban kotu bi sa umarnin mai gabatar da kara na gwamnati”.

Hakkin mallakar hoto
Audu Marte

Image caption

Wasu ‘yan sandan Najeriya sun yi zanga-zanga a Maiduguri a kwanan baya

Malam Sulaiman ya kara da cewa,”Amma abin mamaki sai ya kasance babu jituwa tsakanin ‘yan sanda da wadanda ya kamata ya tsare. Daman kullum wanda ake cuta ba shi da abokin gaba sai mai cutarsa”.

Ya shaidawa BBC Hanyar da ya kamata abi dan magance matsalar ta hanyar bai wa ‘yan sanda kayan aiki na zamani, da tabbatar da ba su horo dan su kware a aikinsu.

A debi mutane aiki yadda ya kamata, duk wanda bai yi aikinsa yadda ya dace ba to a hukuntashi da raba shi da aikin hakan zai sanya a rage matsalolin tsaro.

Haka kuma samari da ‘yan mata da suka gama karatu su samu ayyukan yi, ba lallai sai na gwamnati ba ko daga hukumomi masu zaman kansu ta hakan za a rage zaman banza da ke kawo yaduwar aikata muggan laifuka tsakanin al’uma.Source link

Sheikh Sani Yahaya jingir yayi kira ga ‘yan siyasa da su hada kai da shugaba Buhari


Shehin malamin addinin Islama, Sani Yahaya Jingir yayi kira ga ‘yan siyasa da su hada kai da shugaban kasa Muhammadu Buhari dan ci gaba da ayyukan raya kasa.

Jaridar Rariya ta ruwaito malamin yana cewa:

Ina Kira Ga ‘Yan Siyasa Nagari Da Su Hada Kai Da Buhari Domin A Cigaba Da Gudanar Mana Da Ayyukan Ci Gaba A Kasar Mu Nijeriya.Source link

An dage wa AC Milan haramcin buga gasar Europa


An dage haramcin shekara daya na buga wasannin gasar Turai a kan AC Milan.

Hukumar Uefa ce ta zartar da hukuncin a kan Milan saboda ta keta dokar cinikin ‘yan wasa bayan ta kashe fan miliyan dari biyu a kasuwar musayar ‘yan wasa.

Amma kotun wasanni (Cas) ta yi watsi da hukuncin inda ta amince da karar da AC Milan ta daukaka.

Yanzu hukuncin kotun ya ba AC Milan damar buga wasannin gasar Europa League a bana.

An kammala Seria A, Milan tana matsayi na shida, wanda ya ba ta damar buga matakin rukuni na gasar Europa League.

Yadda hukuncin yake tun farko

Kulub din ya kasance mallakin tsohon Firaministan Italiya Silvio Berlusconi daga 1986 kafin sayar wa wasu ‘yan China kan yuro miliyan 740 a watan Afrilun 2017.

A lokacin kulub din ya kashe fan miliyan dari biyu wajen sayen ‘yan wasa, da suka hada da Leonardo Bonucci daga Juventus da Andre Silva daga FC Porto.

Kotun wasanni ta ce duk da cewa hukuncin Uefa ya yi daidai amma ya kasa cimma wasu sharudda wadanda ya kamata a yi la’akari da su.

Cas ta ce arzikin kulub din yanzu ya fi na da.

An dai bullo da dokar kashe kudi wajen sayen ‘yan wasa domin kaucewa durkushewar kungiyoyin kwallon kafa a Turai.

Kulub na iya fuskantar hukunci idan da ya kashe kudi fiye da adadin kudaden da yake samu.

Hukuncin ya shafi gargadi ko rage maki ko kuma takunkumin sayen ‘yan wasa.

bbchausaSource link

Kotu ta daure tsohon minista a Zimbabuwe | Labarai | DW


Wata kotu a Zimbabuwe ta yanke wa tsohon ministan makamashin kasar hukuncin zaman shekaru hudu a kurkuku, bayan da ta sameshi da hannu a badakalar cin hanci a tsohuwar gwamnatin shugaba Robert Mugabe.

A yanzu tsohon ministan Samuel Undenge mai shekaru 62 da haihuwa zai shafe shekaru biyu da rabi a daure, bayan da ya yi shekara guda da rabi a kan zargi ba da kwangilar makudan kudade ta bayan fage.

Wannan dai shi ne karon farko da aka cimma nasarar daure wani daga cikin jiga-jigan jami’an tsohon shugaban kasar Mugabe. Gwamnatin shugaba Emmerson Mnangagwa ta yi aniyar sa kafar wando guda da ayyukan cin hanci da rasha, sai dai ‘yan adawa na sukar tafiyar hawainiya a cika alkawarin yaki da cin hancin.Source link

Karanta labarin kakar Obama dake addinin musulunci


Sarah Onyango Obama wata Kakar tsohon Shugaban Kasar Amurka Barack Obama ce da ke zaune a Kasar Kenya. A kan kira wannan tsohuwa mai shekaru 86 a Duniya da Sarah Ogwel Obama ko kuma Sarah Hussein Obama a wani lokacin.

Wannan Baiwar Allah da har yanzu tana raye a Kassr Kenya, Kishiyar Kakar Obama ce. Barack Obama wanda asalin Iyayen su Mutanen Kasar Kenya ne ya zama Bakin farko da ya mulki Kasar Amurka inda ya kammala wa’adin sa a farkon 2017.

Miss Onyango Obama Malamar Makaranta ce asalin ta kuma ta kan taimakawa Marasa karfi a Yankin ta. Sarah Ogwel Obama tana zaune ne a a Garin Nyan’oma Kogela wanda ke kusa da babban Birnin Kisumu da ke Yammacin Kasar Kenya.

Tsohon Shugaban Kasar Amurkan Obama ya kan kira ta ne da Goggo Sarah watau Sarah Granny. Sai dai ita ba ta iya Ingilishi ba don haka sai an nemi tafinta idan za ta zanta da jikan ta Obama. Sarah Obama ta na jin yaren Luo ne na mutanen Kenya.

A 2008 lokacin Obama na neman mulki, ‘Yan adawa sun yi ta kokarin nunawa Duniya cewa shi Musulmi ne ‘Dan Afrika domin kuwa Kakannin sa Musulmai be. Sarah Obama dai har yau ta na yin sallah da sauran ibada na addinin Musulunci.Source link